Tunisia na son zawarcin Champions League na Afirka

Tunisia

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafar Tunisia ta zama ta baya-bayan nan da ta nuna bukatar karbar bakuncin wasan karshe a gasar Zakarun Afirka ta Champions League.

Tunisia ta bayar da sanarwar aniyarta ranar Alhamis 20 ga watan Fabrairu lokacin da aka ajiye ka'idar rufe karbar takardun takara.

Morocco ta mika bukatar karbar wasan karshe a gasar Champions League da za a yi 29 ga watan Mayu da na Confederation Cup da za a buga 24 ga watan na Mayu.

Sai dai ita Tunisia wasan karshe na kofin Zakarun Afirka na Champions League take son karbar bakunci kadai.

Ita kuwa Afirka ta Kudu ta bai wa hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF da ta zaba mata karawar da za ta ba ta tsakanin gasar Champions League ko kuma Confederation.

Kungiyoyin Tunisia biyu sun kai wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League na bana da ya hada da Esperance da kuma Etoile du Sahel mai rike da kofi.

Babu wata kungiya daga Tunisia da ta rage a Cnfederation Cup, bayan da tun a farkon gasar bana aka yi fatali da CS Sfaxien da kuma US Ben Guerdane.