Messi ya yi kaca-kaca da Eibar

.

Asalin hoton, Getty Images

Lionel Messi ya zura kwallo hudu rigis a wasan da Barcelona ta yi kaca-kaca da Eibar, abin da ke nufin ta ci wasa hudu a jere a gasar La Liga.

Hakan ya zama tamkar matsin lamba ga abokiyar hamayyarta Real Madrid.

Messi ya zura kwallo uku a minti 26 na zagayen farko kuma ya kara kwallo guda bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a yayin da Martin Braithwaite ya yi yunkurin hana shi cin kwallon.

Arthur ya zura kwallo ta biyar minti biyu bayan haka.

Yanzu Barcelona ta bai wa Real Madrid, wacce za ta fafata da Levante, tazarar maki biyu.

Bayan soma wasan cikin sanyin kafa, Messi ya zura kwallon farko ne bayan da ya yi gare da kwallon inda ta tsallake mai tsaron gidan Eibar wato Marko Dmitrovic minti 14 da fara murza leda.

A yayin da ake shirin tafiya hutun rabin lokaci, Messi ya doki kwallon daga gefe sannan ya zura ta.

Eibar ta ci gaba da yin gumurzu da aka dawo daga hutun rabin lokaci, inda aka hana dukkan kungiyoyin wasu kwallaye da suka zura saboda sun ci su ne daga yankin da aka haramta zura kwallo, ko da yake daga bisani Messi ya zura kwallonsa ta hudu sannan Arthur ya ci kwallo ta biyar.

Ranar Talata Barcelona za su fafata da Napoli a wasan 'yan 16 na cin Kofin Zakarun Turai, kuma daga bisani za su je Bernabeu domin karawa da Real Madrid ranar Lahadi.