Rasha ta musanta zargin yada karya a intanet kan coronavirus

A security guard wears a mask in Beijing

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Claims circulating online allege the virus is an attempt to wage an "economic war on China"

Rasha ta karyata Amurka kan zargin da Amurkan ke mata na yada bayanan kanzon kurege game da cutar coronavirus a kafofin sada zumunta.

Gwamantin Amurka na zargin wasu shafukan sada zumunta masu alaka da Rasha da yada bayanai marasa tushe cewar Amurka ce ta kirkiro annobar cutar.

Jami'an Amurkan sun ce dubban shafukan Twitter da Facebook da Instagram na ta yada labarin na bata suna.

Sakonnin sun kuma zargi daya daga cikin shugabannin kamfanin Microsoft na Amurka, Bill Gates da hannu a annobar.

Rasha ta yi watsi da zargin a matsayin shaci fadi. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar, Tass cewa, "zargin karya ce tsagwaronta.''

Mutum fiye da 2,000 sun mutu, yawancinsu a Chana, ta dalilin kamuwa da coronavirus mai sarke hanyoyin numfashi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Maria Zakharova ta yi watsi da zargin da jami'an gwamnatin Amurka suka yi a matsayin ''karya''

Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka Philip Reeker, ya zargi wasu 'miyagu' daga Rasha da yada bayanan karya game da asalin kwayar coronavirus.

A cewarsa, dabarun sun hada da yada karairayi a intanet cikin harsuna cewa cutar makami ne ''na karya tattalin arzikin Chana".

''Da hakan, 'yan Rashan na neman yin barazana ga lafiyar al'umma ta hanyar kokarin kawar da hankali daga matakan da duniya ke dauka a kan cutar," inji Phillip.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Fiye da mutum 2,000 sun rasu yawancinsu a kasar Chana

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ce a farkon watan Janairu ne jami'an sa ido na Amurka suka fara gano irin wadannan sakonni, bayan mutuwar mutum na uku ta sanadiyyar coronavirus.

An gano cewa shafukan na da hannu a yada bayanai da sakonnin da Rasha ke goyon baya, ciki har da zanga-zangar Chile da yakin Syria.

Gwamnatin Amurka na zargin sakonnin sun sa wasu kasashen Afirka sanya ayar tambaya a kan kasashen yammacin duniya.

Gidan talabijin na Rasha ya sha bayar da rahotannin da ke dora laifin cutar a kan masu karfin fada a ji na yammacin duniya, musamman Amurka.

Gidan Talbijin na Channel One na gabatar da wani sharhi na musamman a kan coronavirusa wanda ke zargin manyan mutane - kamfanonin hada magunguna da kuma gwamnatin Amurka da jami'anta - da hannu a kirkirar kwayar cutar da yaduwarta ko kuma sanya fargaba game da ita