Shugaban Ghana na neman tazarce

.

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya yanki tikitin sake tsayawa takarar shugabancin kasa a karo na biyu, a karkashin jam`iyya mai mulki ta NPP.

Ya kuma bayyana Dakta Mahamudu Bawumia a matsayin mataimakinsa idan jam`iyyar ta zabe shi a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zaben 2020, wanda za a gudanar nan da `yan watanni masu zuwa.

Gangar siyasa dai za a iya cewa ta fara kadawa a kasar, ganin yadda 'yan takara ke ta shirye-shiryen tunkarar babban zaben kasar.

Tuni dai jam`iyya mai mulki a kasar ta fara cika bakin cewa, babbar jam`iyyar hamayya ta NDC ta karaya, saboda sake tsayawa takarar shugaban da mataimakinsa a wa`adi na biyu.

Sai dai a nasu bangaren, babbar jam'iyyar adawa ta NDC ta mayar da martani dangane da wannan ikirari na NPP mai mulki inda suka ce wannan ba maganar saurare ba ce.

Tuni dai masana harkokin siyasa suka fara hasashen yadda za a yi kan-kan-kan a zaben na shugaban kasa musamman tsakanin manyan jam'iyyun siyasar Ghana wato NPP da NDC.

Wasu da dama kuma na fargabar cewa za a iya samun yamutsi, duba da yadda aka samu tashin tashina a lokacin wani zaben ciki gurbi.

Sai da kuma a wani bangaren, har yanzu tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama bai zabi mataimakinsa ba tukuna, duk da cewa ya dade da samun tikiti a babbar jam'iyyar ta NDC a zaben shugabancin kasa mai zuwa