Kante ba zai buga wa Chelsea wasan Bayern ba

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

N'Golo Kante ba zai buga wa Chelsea wasan farko zagaye na biyu a gasar Champions League da za ta buga da Bayern Munich ranar Talata ba.

Ana sa ran dan kwallon tawagar Faransa zai yi jinyar mako uku, kafin ya koma fagen fama.

Haka ma da kyar ne idan 'yan wasan Chelsea Christian Pulisic da Pedro da kuma Callum Hudson-Odoi za su iya yin gumurzun.

Sai dai kuma Ruben Loftus-Cheek ya koma kan ganiya, har ma ya yi zaman benci a fafatawar da Chelsea ta doke Tottenham a gasar Premier ranar Asabar.

Shi kuwa dan wasan Bayern mai tsaron baya Niklas Sule da kuma Ivan Perisic ba za su buga wasan na Stamford Bridge ba.

Watakila Javi Martinez ya buga wa kungiyar Jamus karawar, bayan da a baya bai buga mata wasa shida ba, sakamakon jinya.

Chelsea ta kawo wannan matakin bayan da ta yi ta biyu a rukuni na takwas da maki 11, ita kuwa Beyern ita ce ta ja ragamar rukuni na biyu da maki 18.

Wannan ne wasa na na biyar da za su fafata a gasar cin kofin Zakarun Turai kuma karawa ta hudu a Champions League.

Kowacce kungiya ta ci wasa daya, sannan suka yi canjaras biyu a wasannin cin kofin Zakarun Turai.

Chelsea ba ta taba yin rashin nasara a gasar Champions League da kungiyar Jamus a Stamford Bridge ba.

Cikin fafatawa tara da ta yi da kungiyoyin Jamus a gida ta ci wasa shida da canjaras uku, kuma ba a zura mata kwallo ba a karawa shida.

Chelsea tana ta hudu a teburin Premier za kuma ta karbi bakuncin Munich da kwarin gwiwa, bayan da ta ci Tottenham 2-1 ranar Asabar.

Ita kuwa Bayern tana ta daya a teburin Bundesliga da maki daya tsakaninta da RB Leipzig ta biyu.

Bayern Munich ta lashe kofin Champions League biyar a tarihi, ita kuwa Chelsea tana da shi guda daya da ta dauka a kakar 2011/12.

Karawar da aka yi tsakain Chelsea da Munich:

2013/2014 UEFA Super Cup

  • 30 ga watan Agustan 2013Bayern Munich 2 - 2 Chelsea

2011/2012 CHAMPIONS LEAGUE

  • Asabar 19 ga watan Mayun 2012 Bayern Munich 1 - 1 Chelsea

2004/2005 CHAMPIONS LEAGUE

  • Talata 12 ga watan Afirilun 2005 Bayern Munich 3 - 2 Chelsea
  • Laraba 6 ga watan Afirilun 2005 Chelsea 4 - 2 Bayern Munich