'Abin da ya sa gwamnatin Najeriya ta kwace kaddarorin Buba Galadima'

Bayanan sauti

'Abin da ya sa aka kwace gidan Buba Galadima'

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hirar da BBC ta yi da Buba Galadima:

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta umarci hukumar da ke sanya ido kan masu taurin bashi AMCON a kasar ta kwace wasu kaddarorin Buba Galadima.

Kotun ta ba da umarnin ne saboda tarin bashin da AMCON take bin fitaccen dan siyasar da suka kai kusan N900m.

Cikin sanarwar da AMCON ta fitar, ta ce Buba Galadima ya karbi rancen ta hannun Unity Bank a shekarar 2011 kuma tun lokacin, hukumar ta yi kokarin ganin an samu maslaha.

mma Galadima da kamfaninsa Bedko Nigeria Limited sun gaza biyan kudaden da hukumar ta ke binsu, a cewar sanarwar.

Umarnin kotun wanda mai shari'a A.I Chikere ya zartar da shi ya bai wa hukumar damar ta kwace ragamar kadarorin na dan siyasar.

Kadarorin da aka kwace sun hada da gida mai lamba 15 a Addis Ababa Crescent da ke Wuse Zone 4 a babban birnin kasar da kuma gida mai lamba 4 a Bangui Street, Wuse 2 shi ma a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban AMCON, Jude Nwauzor ya ce hukumar za ta dauki duk matakan da suka kamata kan kamfanin Bedko Nigeria Limited da kuma daraktocinsa bisa hukuncin kotun da kuma dokokin hukumar da aka yi wa gyran fuska.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai tuni Buba Galadima ya mayar da martani inda ya fada wa BBC cewa wannan lamari na da nasaba da takaddama kan wani bashin banki wanda ya shafi wata kwangilar sayen taki da gwamnatin jihar Kano ta ba shi a shekarar 2003.

Ya ce "Ni ne na samu kwangila ta kawo taki a zamanin Gwamna Ibrahim Shekarau a 2003, da aka bani kwangila na je bankin Tropical Commercial Bank na nemi a bani kudi bashi na kawo kayan.

"Ban karbi kudi a wajensu ba, kudinsu yana gunsu, duk inda na je neman kaya sai a ce ba za a karbi takardar bashi daga bankin ba domin bankin ya na da matsala da hukumar Amurka," in ji Buba Galadima.

Ya kara da cewa: "An yi haka har shekara uku, ni ban karbi ko kwabo ba, su ake bude takardar bashi a wurinsu, a dalilinsu ne aka ki karbar kudin nan domin ai ba wanda za ka je wurinsa yana da kayan sayarwa da kudinka, ya hana ka."

Ya ce daga baya bankin Tropical ya aiko masa da bill cewa kudin ruwa ya taru na naira miliyan 349 "suka tafi kotu a kan a tilasta ni na biya wadannan kudade."

A cewar fitaccen dan siyasar, "Babu abin da na bayar ajiya idan an biya saboda yarjejeniyarmu da shi shi ne idan kaya ya zo za a biya kudin kayan ta hanyarsu, tun da kaya bai zo ba, shi ne suka shigar da kara cewa na biya kudin."

Buba Galadima ya ce bayan sun shigar da kara a kansa sannan rashin gamsuwa da hukuncin kotun ya sa ya garzaya kotun daukaka kara kuma kotun ta ce hukuncin farko "ba daidai ba ne."

Ya ce tun da ya daukaka kar yau shekara guda ke nan amma "bankin sai ya ki zuwa Kotun Koli don daukaka kara, sai ya je babbar kotu wadda kuma ta yanke wannan hukunci aka yin min wulakanci. Aka kore ni daga gidana da ni da mutane fiye da 40 da muke kwana, yanzu kila yau mu kwana a kan titi."