EFCC ta kama dan majalisar dokokin Kano saboda almundahana

EFCC ta ce Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi Hakkin mallakar hoto Kano asssembly
Image caption EFCC ta ce Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi

Hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC ta ce ta kama tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar yanzu Isiyaku Ali Danja.

Wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban sashen yada labaranta, Tony Orilade, ta ce an kama shi ne bisa zarginsa da yin amfani da ofishinsa ba yadda ya kamata ba da kuma sace wasu kudade da aka ware domin ayyukan mazabu.

Hukumar ta dauki matakin ne sakamakon wata takardar korafi da aka shigar cewa an karkatar da wasu kudaden haraji da suka kai sama da N1.5b daga asusun gwamnatin jihar Kano.

Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi.

Sai dai a sanarwar EFCC ba ta bayyana sunan wanda ya shigar da karar ba.

EFCC ta ce za ta shigar da kara gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

A makon jiya ma, EFCC ta kama kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano, Mukhtar Ishaq, bisa karkatar da wasu kudaden karamar hukumar birni lokacin da yake shugaban karamar hukumar.