Afghanistan: Shugaba Ghani ya yi watsi da batun sakin 'yan Taliban

Mayakan Taliban

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mayakan Taliban fiye da 10,000 ne aka kiyasta suke tsare a gidajen yari a Afghanstan.

Gwamnatin Afghanistan ta yi watsi da batun sakin mayakan Taliban 5,000 kamar yadda aka yi alkawari tsakanin kungiyar da Amurka.

Shugaba Ashraf Ghani ya bayyana haka ne kwana daya bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Afghanistan tsakanin Amurka da Taliban.

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin Amurka da Taliban a Qatar, ta yi tanadin sakin mayakan kungiyar 5,000.

Ita kuma kungiyar za ta sako wa gwamanti mutum 1,000 kafin ranar 10 ga watan Maris da muke ciki.

Yarjejeniyar ta kuma shardanta janye sojojin Amurka a hankali daga kasar bayan sun shafe shekara 20 a cikinta.

Ita kuma Taliban za ta ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da gwamantin Afghanistan sannan ta dakile hare-hare a yankunan da ke karkashinta.

Amma shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya ce gwamantinsa ba ta da hannu a yarjejeniyar, kuma bai kamata sakin fursunonin yaki za zama sharadi a karkashin yarjejeniyar ba.

Ashraf Ghani ya ce batun sakin fursunoni ba hurumin Amurka ba ne, sai abin da mutanen kasar suka ga ya fi dacewa.

Ya ce idan ma za a yi batun, to sai dai a matsayin fahimtar juna tsakanin bangarorin, amma ba a matsayin sharadi ba.

Dakarun Amurka sun fara kai mamaya ne a Afghanistan a 2001 bayan kungiyar al-Qaeda da ke kasar a lokacin ta kai wasu munanan hare-hare birnin New York na Amurka.

Ayyukan sojin Amurka da kawayenta a Afghanistan sun hambarar da gwamnatin Taliban, wadda ta rikide zuwa kungiyar 'yan tawaye, kuma take da tasiri a kashi biyu bisa ukun kasar har zuwa 2018.