Zanga-zangar 'yan Katolika kan matsalar tsaro a Najeriya

Zanga-zangar 'yan Katolika kan matsalar tsaro a Najeriya

A baya cocin ya bukaci mabiya su sanya bakaken kaya domin nuna juyayi game da matsalar.

Najeriya na fama da matsalar tsaro da dama.

A baya masu garkuwa da mutane sun kama wasu mambobin cocin.

Wasu sun mutu wasu kuma an sako su bayan an biya kudin fansa.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana yin iya kokarinta domin magance matsalar.