Dalilai 5 da suka sa aka yi nasara a kan Liverpool

.

Asalin hoton, Getty Images

A daidai lokacin da Jurgen Klopp yayi kokarin nuna kwazon kungiyarsa ta Liverpool a filin wasan Watford, abin ya ci tura ganin yadda aka yi wa kulob dinsa kaca-kaca.

'Yan jarida kusan 100 ko fiye da haka ne suka taru a filin wasa na Vicarage Road da niyya guda daya kacal - Liverpool na gab da sake kafa tarihi a Premier da nasarar da za ta samu a kan Watford ta 19 a jere.

Bayan an tashi wasan, kocin Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana cewa "3-0 ta dan yi yawa amma duk da haka mu ne a sama".

Ga dalilai biyar da suka jawo wa Liverpool din ta sha kashi:

Tsoron ficewa daga Premier

Kafin wasan na jiya, Watford tana ta 18 a kasan teburi da maki 20, ma'ana tana cikin 'yan ukun da ke kokarin sauka daga gasar Premier zuwa ta Championship.

Kamar yadda aka sani, babu kungiyar da za ta so ta fice daga babbar gasa zuwa karama, abin da ya sa kenan 'yan wasan Watford suka zage dantse suka bai wa magoya baya abin da suke son gani.

Nasarar ta sa ta koma saman Bournemouth a mataki na 17 da tazarar kwallo daya tak.

Asalin hoton, Getty Images

Baraka a bayan Liverpool

Dejan Lovren bai buga wasan Premier tun 7 ga watan Disamba ba sannan kuma Joe Gomez bai buga wasan ba saboda rashin kwarin jiki. Saboda haka ne Lovren ya gaza yin kai kawo domin dakile hatsabibancin Ismaila Sarr, wanda ya zira kwallo har biyu a ragar jajayen.

Shi kansa babban bango Virgil van Dijk ya yi kura-kuran da ba a saba gani ba sannan kuma Fabinho ma kwallo ta rika zirare masa a tsakiyar fili. Ba haka aka saba gani ba a tsakiyar Liverpool.

Kwarin gwiwa daga magoya baya

Kafin take wasan, magoya bayan Watford ba su zauna jiran tsammanin abin da zai faru da tawagarsu ba kamar sauran, wadanda Liverpool ta doddoke a baya, sun kasance masu imanin cewa za su iya doke Liverpool duk da cewa alamu ba su nuna hakan ba duba da yadda suka buga wasa biyar a jere ba tare da nasara ba na baya-bayan nan a Premier.

Sun yi ta ingizawa tare da karfafa wa tawagarsu gwiwa ba tare da la'akari da kuskure ba - lokacin da Sarr ya tsinke a guje a farkon wasan sun yi ihu sosai wanda ya girgiza 'yan wasan baki dayansu.

Asalin hoton, Getty Images

Salah, Firmino, Mane - kamar babu su a wasan

'Yan ukun da suka fi kowadanne kokari a manyan gasa biyar na nahiyar Turai wato Mohammed Salah da Sadio Mane da kuma Roberto Firmino ba su yi kokari ba a wasan kwatakwata.

A cikinsu duka, Salah ne kadai ya buga shot biyu kuma dukansu babu na-ci wato on target, hasali ma daya daga ciki bai je ko'ina ba aka tare shi.

Watford ta buga shot 14, inda Liverpool ta buga 7. Watford ta kirkiri dama 13, Liverpool 5 kacal ta kirkira.

Liverpool ta manta yadda ake rashin nasara

Rabon da a ci Liverpool a kowace gasa tun 17 ga watan Disamban 2019 (Aston Villa 5-0 Liverpool, Carabao Cup) kafin kuma Athletico Madrid ta doke ta ranar Talata 18 ga Fabarairu a Champions League. Kazalika ba a ci ta ba a Premier baki daya. 

Saboda haka, a iya cewa Liverpool ta manta yadda ake yin rashin nasara a wasa ko kuma abin da rashin nasara ke nufi ma ba ki daya. Hakan ya taka rawa musamman ganin yadda abokan hamayyarta suka sha fama da sauye-sauyen koci da sauransu.

Wannan rashin nasara na nufin har yanzu Arsenal ce kungiyar da ta taba lashe gasar Premier ba tare da an doke ta ba a tarihi a shekarar 2003-2004.

Har yanzu Liverpool ce a saman teburi da maki 79, yayin da Man City ke biye mata da maki 57 da kwantan wasa daya, sai kuma Leicester da Chelsea a matsayin ta uku da ta hudu.