Yadda mabiya Darikar Katolika suka yi zanga-zanga a Abuja

.

Mabiya Darikar Katolika a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna alhini da neman mafita daga matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Zangar-zangar ta 'yan Katolika zalla da aka gudanar a babban birnin kasar Abuja ya samu halarcin daruruwan mabiya da limaman darikar.

Tattakin da suka fara tun daga Babban Cocin Kasar ya hada addu'o'in samun zaman lafiya da tsaro a kasar, tare da neman gwamnati ta dauki matakan da suka dace wurin magance matsalar.

Bayanan bidiyo,

Tattakin nuna damuwa game da rashin tsaro a Najeriya

A bayan ma cocin ya jagoranci gudanar da irin wannan zanga-zanga a shekarar 2018, sai dai na 2020 ya fi samun tagomashi da yawan mahalarta.

Cocin ya koka bisa yadda mambobinsa suka fada hannun masu satar mutane inda aka kashe wasunsu, sannan aka sako wasu bayan biyan kudaden fansa.

Ko a ranar Laraba ma cocin ta umarci mabiyanta a fadin Najeriya su sanya bakaken kaya domin nuna bakin ciki kan kashe-kashe da ke shafar mabiyansa.

Larabar ce dai ta kasance Ranar Toka a addinin kiristanci, wacce kuma ita ce ranar farko ta azumin kwana 40 da Kiristocin suke yi.

Zanga-zangar ta ranar Lahadi na daga irin damuwar da mabiya Darikar Katolika suke nunawa da kuma neman hukumomi su dauki mataki kan matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fama da ita.

A nata bangaren, gwamnatin kasar na cewa tana iya kokarinta wajen tunkarar matsalar.