Turkiyya ta kakkabo jiragen yakin Syria

Yaki ya kazanta a Arewacin Syria tun bayan kashe wasu sojojin Turkiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaki ya kazanta a Arewacin Syria tun bayan kashe wasu sojojin Turkiya

Turkiyya ta kakkabo jiragen yakin Syria guda biyu ranar Lahadi bayan Turkiyyar ta tsananta kai hare-hare a Arewacin Syria.

Matukan jiragen sun yi saukar lema domin tsira da rayukansu a Idlib inda sojin Turkiya da 'yan tawaye ke gwabza yaki da dakarun Syria.

Turkiyya mai goyon bayan 'yan tawayen Syria, ta ce ta kai hari a kan motocin yaki da na'urorin kakkabo rokoki na gwamnatin Syria.

A makon da ya gabata ne yakin ya fara yin tsanani a Idlib bayan an kashe sojan Turkiyya 33 a wani harin sama.

Lamarin ya haddasa fargaba game da yiwuwar kazancewar yaki tsakanin Turkiya da Rasha, babbar kawar Syria.

Amma a ranar Lahadi, Ministan Tsaron Turkiya Hulusi Akar ya ce kasarsa ba neman fada da Rasha take yi ba.

"Muna neman Rasha ta hana gwamnatin Syria kai hare-hare ne," a wani sako da ya bayar ta talbijin. "Ba mu da nufi yin fada da Rasha."

Mista Akar ya ce hare-haren sojin kasarsa sun lalata jirgi maras matuki da jirage masu saukar ungulu 8 da tankokin yaki 103, baya ga bindigogin harba rokoki da sauran kayan yakin Syria.

A cewarsa, dakarun kasarsa sun kuma yi gabalaba a kan sojoin Syria 2,212.

Kungiyar sa ido ta Syrian Observatory ta ce an kashe sojojin gwamnati da mayakan sa kan Syria 27 tun daga ranar 27 ga watan Fabrairu.