Tottenham na son sayo Smalling

Chris Smalling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Smalling na zaman aro a Roma

Dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho baya tunanin inda zai koma, duk da alakanta shi da komawa Manchester United ko Liverpool. (Mail)

Tottenham za ta nemi mai tsaron ragar Watford Ben Foster wanda yarjejeniyarsa da kungiyar za ta kare bana. (Sun)

Haka ma Tottenham din na fatan ganin ta shiga gaban Roma wurin sayen mai tsaron bayan Manchester United Chris Smalling. Yanzu haka Smalling mai shekaru 30 na zaman aro a Roma. (Calciomercato, in Italian)

Manchester United na sahun gaba cikin masu son sayen mai tsaron bayan Napoli na Italiya Kalidou Koulibaly. Real Madrid da PSG ma na neman dan kasar Senegal din mai shekaru 26. (Express, via Corriere dello Sport)

Mai horar da 'yan wasan Arsenal Mikel Arteta ba zai samu kudi mai yawa ba wurin sayen 'yan wasa, idan kungiyar ta kasa zuwa gasar zakarun turai a badi a yayin da tahotanni ke cewa Arsenal ta kasa samun ribar a zo a gani a bana. (Goal)

Shugaban kungiyar Inter Milan Giuseppe Moratta na tunanin ba za a kammala kakar wasannin bana ba, idan har ba a samu mafita kan yaduwar cutar coronavirus ba. (Mail).

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola ya ce ba za a iya ja da kungiyarsa ba idan ana maganar lashe kofunan cikin gida.

Hakan na zuwa bayan kammala wasan karshe na kofin Carabao inda City ta doke Aston Villa da ci 2-1 a filin Wembley. (BBC).