Kun san asalin jemagun da ke Fadar Sarkin Kano?

Kun san asalin jemagun da ke Fadar Sarkin Kano?

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren karin bayanin da Dakta Sirajo Salisu ya yi kan jemagun Fadar Kano:

Jama'a da dama musamman mazauna Kano a arewa maso yammacin Najeriya ko kuma masu ziyartar birnin, kan yi tambayoyi dangane da dumbin jemagu da ke zaune a kewayen Fadar Kano.

Jemagun dai a kullum sukan yi shawagi da almuru da kuma asuba, kuma duk wanda ya taso a wannan zamanin musamman a Kano ya san da zamansu.

Sai dai jama'a na yawan tambaya dangane da tarihinsu da kuma asalinsu.

Domin haka ne Dakta Sirajo Salisu, wanda malami ne a tsangayar sashen nazarin taswirar yanayin duniya da ke Jami'ar Bayero ta Kano, ya yi karin bayani dangane da wadannan jemagun inda ya bayyana cewa zai yi wuya a kayyade tun lokacin da jemagun suke a fadar ta Kano.

Ya bayyana cewa fadar ta Kano ta kai shekaru kusan 540, tun lokacin Sarki Muhammadu Rumfa.

Dakta Sirajo ya ce gidajen Hausawa a tun zamanin da a kan samu bishiyoyi wanda hakan yake sa ake samun tsuntsaye ko kwari ko dabbobi, domin haka ne za a iya cewa Allah kadai zai iya sanin lokacin da jemagun suka shafe a fadar ta Kano.

Ya ce sarakai har zuwa wannan lokacin sun rike wannan al'adar ta ajiye bishiyoyi a gidajensu.

Dakta Sirajo ya ce jemagun na da alfanu ga su kansu bishiyoyi, inda ya bayyana cewa suna taimaka musu kwarai. Ya ce aman da jemagun suke yi tamkar wani taki ne ga kasa.