Kungiyar Musulmi na son a yi dokar hana bara a Najeriya

.

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar nan mai kare muradun Musulmi a Najeriya MURIC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar haramta gararamba da tallace-tallace ga yara da sunan almajiranci a kasar.

Ta bayyana haka ne bisa wani kiyasi da ta nuna na cewa akwai yara sama da miliyan 10 da ke zaune ba tare da zuwa makaranta ba.

Kungiyar ta MURIC ta ce yawan yaran da ake samu na ta gararamba a titunan kasar wani abu ne da ke sosa mata rai.

A cewar MURIC, yara su ne karfin al'umma, wanda idan aka ba su ilimi mai nagarta, za a ci gajiyarsu.

Kungiyar ta yi kira ga majalisar dokoki ta Najeriya da ta samar da wata doka da za ta rinka hukunta iyayen da ke tura 'ya'yansu gararamba.

MURIC din ta ce hukunta iyaye da suka ki bai wa 'ya'yansu ilimi ko tarbiya mai kyau zai zama darasi ga al'umma.

A wata sanarwa da Farfesa Ishaq Akintola ya aika wa BBC, ya ce nauyi ne a kan iyaye su ciyar da 'ya'yansu da kuma ba su tarbiya ta addini domin dora su a kan hanya bayan sun girma.

Farfesan ya ce ba karamin rashin sanin ciwon kai ba ne iyaye su tura 'ya'yansu kwaroro-kwaroro domin zuwa su roki abinci ko kuma sanya su harkokin aikatau masu wahala.

Kungiyar MURIC ta gargadi iyaye da cewa su ji tsoron Allah domin kuwa, "Allah zai tambaye iyaye daya bayan daya yadda suka kula da 'ya'yansu da kuma tarbiyarsu har zuwa girmansu."

A halin yanzu kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya da kuma gwamnatoci sun fara tashi tsaye domin dakile bara da sunan almajiranci.

Ko a watan Fabrairun da ya gabata sai da gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta haramta bara a titunan jihar.

Sai dai gwamnan jihar ya ce gwamnatin ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga 'yan firamare da sakandare a fadin jihar.