Coronavirus: Saudiyya za ta mayar wa maniyyata aikin Umrah kudadensu

Miliyoyi ne ke ziyartar biranen Makkah da Madinah don gudanar da ibada duk shekara
Bayanan hoto,

Saudiyya ta shiga jerin sama da kasashe 50 da cutar Coronavirus ta bulla

Ma'aikatar kula da aikin Hajji da Umrah a kasar Saudiya ta ce za ta mayar wa maniyyata aikin Umra ko ziyarar kabarin Annabi Muhammad (SAW) kudadensu.

Matakin mayar da kudaden ya zo ne bayan dakatar da aikin ibada da hukumomin kasar suka yi a matakin wucin gadi.

Fargaba kan bazuwar cutar coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya ce ta sanya kasar daukar wannan mataki.

Saudiyya na daga cikin jerin kasashe na baya bayan nan da suka tabbatar da bullar cutar Coronavirus a kasashensu.

Mutun na farko da aka samu da cutar a Saudiyya ya shigo da ita ne bayan tafiya Bahrain da Iran.

Yan kwanakin da suka wuce ne Saudiyya ta dauki matakin dakatar da yan kasashen waje shiga kasar domin gudanar da ibadar Umrah a biranen Makkah da Madinah.

Wasu da suka riga suka biya kudadensu don zuwa ibadar Umrah a Najeriya sun fadawa BBC cewa al'amarin baiyi musu dadi ba ko kadan.

Amma sun bayyana cewa sun rungumi kaddara la'akari da cewa dole ce tasa hukumomin Saudiyya daukar wannan mataki.

Miliyoyin musulmi ne ke zuwa aikin Hajji da Umra da kuma ziyara duk shekara.