'Yan sanda sun kama matar da ta yi safarar yara 23

'Yan sanda

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Rundunar 'yan sanda a jihar Taraba da ke Najeriya ta kama wata mata da ake zargi da yin safarar kananan yara 23.

'Yan sandan sun kama Mary Yakubu wadda ake zargi da safarar yara a tashar motar gain Bali yayin da take kokarin sa yaran a mota zuwa wani waje da ba a sani ba.

Mai magana da yawun rundunar a jihar David Misal ya ce sun kama matar ne saboda "ba ta da kungiya mai zaman kanta sannan kuma ba ta da gidan marayu, kuma ba ta da lasisin da ya ba ta damar daukan yara kanana kuma tun da ba ta da goyon bayan shari'a, ta aikata laifi."

Madam Mary dai malamar aji daya ce a makarantar firamare da ke karamar hukumar Bali kuma daga Balin ne ta kwashi yara 23, wasu daga cikin yaran 'yan gida daya ne.

Misal ya ce matar ta je ta samu iyayen yaran da sunan za ta nemowa "'ya'yansu makaranta mai kyau" amma ba ta fadi sunan mutanen da za su koyar da yaran ba.

Kawo yanzu dai rundunar 'yan sandan ta tuntubi bakwai daga cikin iyayen yaran da suka tabbatar da cewa sun bai wa Madam Mary 'ya'yansu saboda makarantar ba ta kauyensu kuma sun yarda cewa dama ce ga 'ya'yansu su je makaranta.

Iyayen yaran sun ce "ba su karbi kudi daga hannunta ba, sannan ita ma ba ta ba su wani kudi ba."

A yanzu dai an mika yaran 23 hannun ma'aikatar kula da walwalar al'umma da yara da ke jihar, inda za a ci gaba da kula da su.

Sai dai Madam Mary na tsare a hannun 'yan sanda kuma Misal ya ce za su shigar da batun gaban kotu.