Da gaske an gano maganin Coronavirus a Najeriya?

A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cutar Coronavirus ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya yi watsi da ikirarin tsohon Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Maurice Iwu na cewa ya gano maganin cutar Coronavirus.

Dakta Chikwe ya bayyana wa BBC cewa babu yadda za a yi a gano maganin cutar da ba ta dade da bulla ba a duniya.

Ya ce sabuwar cuta ce kuma ba a taba sanin da ita ba ko a fannin lafiya, sai watanni biyu da suka gabata.

Hakazalika ya ce kafin a gane tasirin maganin dole sai an gwada kan marasa lafiya, wanda da yawansu a China suke.

Farfesa Iwu ya yi ikirarin gano maganin cutar ta numfashi, wadda ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma kasarsa Najeriya ta kasance cikin kasashen da cutar ta bulla.

A ranar Litinin Farfesa Maurice Iwu, wanda ke shugabantar cibiyar bincike ta Bio-Resources Institute of Nigeria, ya gana da ministan lafiya da na kimiyya domin neman tallafinsu kan maganin da ya ce ya gano.

Tun da cutar ta bulla a China shekarar da ta wuce, babu wani maganinta da aka amince da shi.

Ya zuwa wannan lokaci, cutar ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma Najeriya tana cikin kasashen da cutar ta bulla.

Sai dai hukumar dakile bazuwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce gwamnati ta shirya gina wurin gwaji da kula da kuma kebe masu cuta a dukkanin jihohin kasar.

A karshe ya ce gwamnatin kasar za ta fitar da wasu ka'idoji domin makarantun da ke sassan kasar.