Coronavirus ta tilasta sauya salon gaisuwa a duniya

Coronavirus ta tilasta sauya salon gaisuwa a duniya

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Tun bayan bullar annobar cutar Coronavirus a sassan duniya daban-daban, wasu mutane suka daina gaisawa da hannu saboda gudun yada cutar.

Wasu sun koma gaisawa ta hanyar hada kafa da kuma sauran sassan jiki.

Cutar ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a duniya tun bayan bullarta a watan Disamban 2019 a kasar China.