Kotun Koli ta kori karar PDP kan zaben Imo

.

Asalin hoton, @EMEKAIHEDIOHA

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP na sake nazari kan hukuncin da ya tumbuke shi.

Hukuncin da kotun ta yanke a baya ya ayyana Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na watan Maris din 2019.

Alkalai bakwai ne karkashin jagorancin Mai Shari'a Tanko Muhammad suka yanke hukuncin inda suka dogara da cewa kotun ba ta da hurumin zama domin ta saurari karar da aka daukaka kan hukuncin da ta yanke a baya game da zaben gwamnan jihar Imo.

Yayin da take karanta hukuncin, Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ta ce bukatar da aka shigar a gaban kotun ba ta da sahihanci don haka kotun ta yi watsi da daukaka karar.

Tun da farko dai Kanu Agabi lauyan PDP da kuma Emeka Ihedioha ne suka bukaci Kotun Kolin ta jingine hukuncin da ta yanke wanda ya bai wa Hope Uzodinma nasarar zama gwamnan jihar.

Ko a makon jiya sai da Kotun Koli a Najeriya ta yi watsi da bukatar da jam'iyyar APC ta shigar na neman ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke wanda ya karbe nasarar da dan takarar jam'iyyar APC David Lyon ya samu a zaben gwamnan jihar Bayelsa inda kotun ta tabbatar da hukuncin da ta yanke wanda ya baiwa Duoye Diri na Jam'iyyar PDP nasara.

Wannan ne ya ja har kotun ta bukaci lauyoyin jam'iyyar APC da kuma David Lyon da suka shigar da karar su biya jami'iyyar PDP naira miliyan 60.