Coronavirus: Hukumar NCDC ta karyata killace shugabanta

.

Asalin hoton, @Chikwe_I

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta karyata wani rahoto da ke cewa an killace shugabanta Dakta Chikwe Ihekweazu kan cutar Coronavirus.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta bayyana cewa tsakanin 16 zuwa 24 ga watan Fabrairun 2020, Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta tura wata tawaga ta musamman zuwa China.

Tawagar na dauke kwararru 25 ciki kuwa har da Darakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya wato NCDC.

Tawagar ta tattauna da kwararru a fannin lafiya a China domin su fahimci matakan da Chinar ke dauka na shawo kan cutar COVID-19.

Hukumar ta bayyana cewa ko bayan da daraktan ya dawo daga tafiya, sai da aka yi masa gwaji aka tabbatar ba shi dauke da cutar ta COVID-19.

Cutar coronavirus ta addabi wasu kasashe a duniya inda a makon da ya gabata ne aka samu bullarta a Najeriya.

Sai dai a wannan makon, kafafen watsa labaran Najeriya sun ambato tsohon shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Maurice Iwu yana ikirarin samo maganin cutar ta coronavirus.

Amma Dakta Chikwe Ihekweazu ya yi watsi da ikirarin tsohon shugaban inda ya bayyana cewa babu yadda za a yi a gano maganin cutar da ba ta dade da bulla ba a duniya.