'Yan sanda sun kwace iko da ofishin jam'iyyar APC

Matakin rufe ofishin na zuwa sa'oi kalilan bayan hukuncin kotu da ya dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Oshimole.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Matakin rufe ofishin na zuwa sa'oi kalilan bayan hukuncin kotu da ya dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Oshimole.

A Najeriya 'yan sanda sun kwace iko da hedikwatar jam'iyya mai mulki ta APC, inda suka girke jami'ansu da dama da kuma motocin domin hana shiga ofishin.

Matakin na zuwa ne sa'oi kalilan bayan wani hukuncin kotu da ya dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Oshiomole.

Yan sanda sun fada wa BBC cewa an basu umarnin su hana kowa shiga komai mukaminsa.

Tsare ofishin baya rasa nasaba da rikicin shugabanci da jam'iyyar ta APC mai mulki ke fama dashi.

Kotu ta dakatar da Adams Oshiomole, bayan karar da wani dan jam'iyyar ya kai cewa tun a bara ne wata kotu ta dakatar da shugaban jam'iyyar, saboda haka babu dalilin da zai sa ya cigaba da jan ragaramar shugabanchin jam'iyyar.

Wannan ba shine karon farko ba da ake samun rahotannin rikicin cikin gida a jam'iyyar APC.

Bangaren da ke goyon bayan mista Oshiomole ya ce babu wanda ya basu takarda a rubuce ba kan matakin.

To amma a cewar sakataren walwalar jama'a na jam'iyyar Ibrahim Masari za su zamo masu biyayya ga abinda kotu tace.

Shima mista Oshiomole ya daukaka kara kan dakatar dashi da kotun tayi.