Harry Kane na son komawa United

Harry Kane
Bayanan hoto,

Yanzu haka Harry Kane yana jinya duk da ana sa ran zai buga gasar Euro 2020

Akwai yiwuwar dan wasan gaban Tottenham Harry Kane ya yanke shawarar komawa Manchester United a kaka mai zuwa (Goal).

Rahotanni na cewa babu alamun Kane zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da Tottenham. (Express).

Arsenal na shirin neman mai tsaron bayan Manchester City John Stones idan an kammala kakar wasannin bana.(90 Min).

Daraktan wasanni a kungiyar RB Leipzig ya ce har yanzu kulob din bai samu wata takardar nuna sha'awar sayen dan wasansa Timo Werner, duk da cewa Liverpool da Chelsea da Manchester United sun nuna sha'awar sayen dan wasan.(Mirror).

Mai tsaron bayan Manchester City Angelino da ke zaman aro a RB Leipzig ya ce zai bar Manchester City matsawar aka tabbatar da cewa ba za ta buga gasar zakarun turai ba a badi.(MEN).

Manchester United na neman dan wasan Birmingham Bellingham. (MEN).

A wata mai kama da haka rahotanni na cewa akwai yiwuwar Dortmund za ta iya bukatar yuro miliyan 140 ga duk mai neman dan wasan gabanta Jadon Sancho. (Bild -in German).

Dan wasan gaban Chelsea Willian ya ce a shirye ya ke ya koma Tottenham mai makwabtaka, a maimakon sake kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyarsa. (OUL).

Bayanan hoto,

Willian

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu rahotanni sunce za'a bukaci Chelsea ta biya fam miliyan 40 idan har tana son sayen mai tsaron bayan Porto dan kasar Brazil Alex Telles don maye gurbin Marcos Alonso. (Sun).

A Spaniya Atletico Madrid za ta nemi dan wasan tsakiyar Barcelona Ivan Rakitic mai shekara 31 a kaka mai zuwa. (Marca -in Spanish).

Everton da West Ham da Wolves na rububin sayen Hirving Lozano da ke wasa a kulob din Napoli na Italiya. (Calciomercato - in Italian).

Tottenham ta yadda Victor Wanyama dan kasar Kenya ya tafi Montreal Impact ba tare da sun biya ko kwabo ba, duk da sun nemi a basu fam miliyan tara a watan Janairu. (Standard).

Barcelona za ta tsawaita zaman mai tsaron ragarta Marc-Andre ter Stergen. (ESPN).

Mai horar da Arsenal Mikel Arteta zai nemi dan kasar Guinea da ke wasa a Olympiacos Mady Camara mai shekaru 23. (Sdna,via Star).

Hakama Arsenal ta sanar da saukakawa 'yan kallo kudin bas, wadanda ke shirin zuwa kallon wasanta da Manchester City da za'a buga mako mai zuwa. (Standard).