Fafaroma ya ki bayyana a bainar jama'a saboda coronavirus

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Filin ibadar safe na papal Masses fayau ya kasance yayin da Fafaroma yake jagorantar ibada ta bidiyo a intanet

Fafaroma Francis ya gaza bayyana a bainar jama'a a dandalin St Peter's domin guje wa taruwar jama'a yayin da ake fargabar yaduwar annobar cutar coronavirus.

Fadar Vatican ce ta bayyana hakan, inda a yanzu haka yake jagorantar ayyukan ibada ta bidiyon intanet.

Filin ibadar safe na papal Masses ya kasance fayau kuma za a ci gaba da yin hakan har zuwa 15 ga watan Maris.

Fafaroma yana fama da mura amma ba coronavirus ba ce.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da mutum dubu 100 ne suka kamu da cutar a fadin duniya kuma sama da mutum 3,000 suka mutu, mafi yawansu a China.

A Najeriya, har yanzu ba a samu rasa rai ba sakamakon cutar, amma ana ci gaba da killace mutane bisa tsoron yaduwarta.

Cutar ta samo asali ne daga yankin Hubie na China, inda tuni wasu kasashe suka kwashe 'yan kasarsu daga birnin Wuhan na yankin.