Dan wasan Arsenal Torreira zai yi jinyar mako 8 zuwa 10

Lucas Torreira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasa 33 Lucas Torreira ya buga wa Arsenal a bana

Ana sa ran dan wasan tsakiya na Arsenal Lucas Torreira zai yi jinyar mako takwas zuwa 10, sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa, inji Arsenal.

Torreira mai shekaru 24, sai da aka fitar dashi a kan gadon daukar marasa lafiya yayin wasan da kungiyarsa ta buga a gasar FA da Portmouth a makon da ya gabata.

Dan kasar Uruguay din ya samu rauni ne sakamakon wata haduwa da suka yi da dan wasan Portmouth James Bolton a minti na 16 da fara wasan.

Torreira wanda ya koma Arsenal daga Sampadoria a watan Yulin 2018, ya buga wa Arsenal wasa 33 a kakar bana.

Wasan Arsenal na karshe a Premier da za ta buga da Watford, an tsara buga shi ne a ranar Lahadi 17 ga watan Mayu, nan da mako 10 masu zuwa.

Wasan karshe na FA za a buga shi a filin wasa na Wembley ranar Asabar 23 ga watan Mayu.