Coronavirus: An dakatar da gasar Serie A a Italiya

A baya bayannan an fara buga wasannin Serie A ne ba tare da 'yan kallo ba.
Bayanan hoto,

A baya bayannan an fara buga wasannin Serie A ne ba tare da 'yan kallo ba.

Firanministan Italiya Giuseppe Conte ya sanar da dakatar da gasar Serie A har zuwa 3 ga watan Afrilu sanadiyyar ci gaba da bazuwar cutar Coronavirus.

Sai dai dakatarwar ba ta shafi wasannin da kungiyoyin za su buga da wasu kasashen waje ba.

A baya bayannan an fara buga wasannin Serie A ne ba tare da 'yan kallo ba.

Mr Conte hakama ya kara sanar da kara tsaurara matakan takaita bazuwar cutar Coronavirus da suka hada da hana duk wani taro a fadin kasar.

Italiya ta zamo kasar da tafi kowace kasa fuskantar ibtila'in cutar Coronavisur a yankin Turai.

Kawo yanzu cutar ta kama mutun 9,000 tare da kashe 450.

An kuma bayyana cewa za a buga wasan Europa League tsakanin Roma da Sevilla ba tare da halartar 'yan kallo ba.

Wasu rahotanni sunce an samu sabani tsakanin masu ruwa da tsaki kan harkar wasannin Italiyar.

Ko a ranar Lahadi an buga wasan hamayya tsakanin Juventus da Inter Milan ba tare da yan kallo sun shiga filin wasan Turin ba.

Ko a Faransa rahotanni na cewa ma'aikatar wasanni ta yanke shawarar kayyade yawan kallon da za su shiga kallon wasa da nufin takaita yaduwar cutar Coronavirus, kuma wata majiya ta ce ba za su wuce 1,000 ba.

Wannan ya hada da wasan zakatun turai da za a buga tsakanin Paris St-Germain da Borussia Dortmund ranar Laraba, inda tuni aka umurci magoya bayan kungiyoyin da su zauna a gidajensu.