Coronavirus: Kalli yadda wurin killace mutane yake a Kano

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Gwamnatin Kano a Najeriya ta ware wani wuri na musamman a garin 'Yar gaya da ke karamar hukumar Dawakin Kudu domin killace mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Hukumomin jihar sun ce wurin zai iya daukar mutum 14 a lokaci daya sannan yana da dakuna bakwai.