Coronavirus: Na tafka asarar miliyoyin naira

Kantin Kwari

Asalin hoton, Getty Images

Wasu 'yan kasuwa a Najeriya na kokawa kan yadda suke tafka asara ta miliyoyin kudi sakamakon rufe iyakoki da hukumomi suka yi domin hana bazuwar cutar sarkewar numfashi ta coronavirus.

Sun ce lamarin na barazana ga harkokinsu na kasuwanci da kuma tattalin arzikin kasa.

Daya daga cikin 'yan kasuwar Rabiu Abdullahi ya shaida wa BBC cewa 'yan kasuwa sun shiga tashin hankali sosai sanadin coronavirus da ta sa aka rufe iyakokin kasar.

Rabi'u Abdullahi, wanda ya ce yana fitar da auduga zuwa China da Bangladesh da Spaniya ya bayyana cewa ya shafe watanni bai fitar da audugar zuwa kasashen ketare ba.

"Rabon da na fitar da kaya tun watan Fabrairu, kusan ma dai an kulle kamfani, sai mu manyan ma'aikata da muke dan zuwa domin duba na'urori kuma leburori mun ba su hutu." in ji dan kasuwar.

A cewarsa, kamfaninsa ya tafka asarar kusan naira miliyan dari biyu saboda "manya-manyan dilolinmu suna Spaniya, idan suka bamu oda, za mu tura musu kuma su zamu turawa takardu,"

"Su kuma a can basu karbi takardun ba, takardun sun isa a birnin Madrid ga kuma matsalar ba a fita kuma kullum kaya darajarsu dada yin kasa take," kamar yadda ya fada.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Matashin dan kasuwar ya ce a yanzu fafutukar da suke shi ne ta yadda za su samu kudadensu su dawo hannunsu ba wai sake yin odar kaya ba.

"Yanzu duk wanda kake mu'amala da shi ta ina za ka tunkare shi yana wannan babbar masifa ka tunkare shi kace akwai oda ko kaya iri kaza kana da bukata? ai ba zai yiwu ba sai ya dauke ka ma baka san kanka ba." a cewarsa.

Ya ce duk da gwamnati ta sha ikirarin tallafawa masu fitar da kaya amma kuma lamarin ba haka yake ba saboda "akwai kaya da na fitar kwanaki bayan an je wannan matsalar ta taso, kamfanin sun rufe,"

"Na rasa yadda zan yi da kayan har na rubuta takarda zuwa babban bankin Najeriya CBN ko zai taimaka mani wannan kayan nawa a san yadda gwamnati za ta taimaka mani ko ta karbi kayan a ajiye a wurin ajiyar kaya a China kafin na samu mai saye, har yanzu ban samu amsa ba." in ji Rabi'u Abdullahi.

Ya kara da cewa irin haka ba ya faruwa a kasashen da suka ci gaba misali "za su shigo su taimakawa dan kasarsu saboda kada kamfaninsa ya (durkushe).

Da yake magana kan rage yawan ma'aikatansa saboda matsalar, Rabi'u ya ce ya bai wa kananan ma'aikata hutu tun watan Fabrairu "amma duk wata idan ana biyanka dubu dari, sai a baka dubu hamsin saboda kaima kana da iyali,"

Dan kasuwar ya kara da cewa a yanzu ya dakatar da kasuwancin auduga har sai yadda hali ya yi.

Ya ce tun auduga tana dubu daya da dari takwas suke fitar da auduga "a yau ta dawo dala dubu daya da dari biyu da hamsin kuma wannan kayan nawa da nace an yi wannan asarar an tura su a wannan farashin,"

"Ka ga kuma abin da ya biyo baya, kokari ake a kwaci kai kudinma ya dawo ba maganar riba ake ba," in ji sa.

Ya kuma yi fata mahukunta a Najeriya za su yi koyi da takwarorinsu na Kamaru ta yadda ake daukar matakan ragewa 'yan kasuwa radadin asarar da suke.

"Akwai kamfanina a Kamaru, manaja na ya kira ni duk da ni ba dan kasa bane an sani amma ina kawo arziki a kasar, suka kirawo ma'aikata na aka rage musu radadi, ko ni aka ragewa kamfanina radadin kudi mai yawa aka biya ma'aikata na albashi na wata biyu,"

"Duk ma'aikacina sai da aka ba shi jaka saba'in-saba'in kudin Kamaru kyauta lura da yadda suke ganin ina fitar da kaya ta tashar jirgin ruwa," kamar yadda dan kasuwar ya bayyana.

Ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta yi nazari kan kamfanonin da suke fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje sannan su duba ko kayayyakin suna da alaka da kasashen da suke rufe.

A cewarsa "Idan kana biyan albashi dubu dari biyu, gwamnati ta rage ma ta dauki dubu dari ta rage ma, za su kara maka kwarin gwiwa ka ci gaba da gudanar da kamfanin."

A ganinsa, rufe iyakoki da gwamnati ta yi abu ne mai kyau domin hana bazuwar annobar coronavirus sai dai ya ce "hakan ya tare harkokinsu kamar baki da suke zuwa daga wasu garuruwan makwabta kamar Katsina da Kaduna da Jigawa ba sa samun damar shigowa jihar Kano - lamarin da ya ce yana shafarsu matuka."