Coronavirus: An tura ma'aikata 3,000 a Kano don yaki da korona

Boss Mustapha

Asalin hoton, Nigeria Govt

Bayanan hoto,

Boss Mustapha ya ce za su shawo kan matsalar a Kano

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tanadi ma'aikata 3,000 a Jihar Kano da za su yi aikin dakile yaduwar cutar korona a jihar.

Shugaban kwamitin gwamnatin tarayya mai yaki da korona, Boss Mustapha ne ya bayyana haka ranar Juma'a a wurin taron manema labarai da kwamitinsa ke yi kullum a Abuja.

Boss Mustapha ya ce wadannan ma'aikata za su shiga cikin al'umma ne a jihar da nufin tattaro bayanan abubuwan da ke wakana a tsakanin jama'a.

Ya kuma ce tun bayan da aka kafa cibiyar gwajin cutar a Kano al'amura suka fara kyautata ta hanyar gano masu dauke da cutar.

"Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na tattara wata tawagar mutum 3,000 daga cibiyoyin lafiya a matakin farko da za ta tattaro bayanai a tsakanin al'umma," a cewar Boss Mustapha.

Asalin hoton, Nigeria Govt

Bayanan hoto,

Kwamitin yaki da korona na aiki domin dakile cutar

Boss Mustapha, wanda har wa yau shi ne sakataren gwamnatin tarayya, ya ce tawagar za ta yi aiki a matakin jiha da na karamar hukuma.

Ranar Laraba kuma wata tawagar likitoci daga gwamnatin tarayya ta isa Kano domin farfado da ayyuka a cibiyar gwajin cutar korona da aka rufe bayan wasu ma'aikatan lafiya sun harbu da cutar.

Ya zuwa daren ranar Alhamis, mutum 219 ne suka harbu da cutar korona a Kano sannan biyar suka mutu.