Eid-al-Fitr: 'Yan Najeriya suna jiran Sallar Idi ranar Lahadi

..

Asalin hoton, Getty Images

'Yan Najeriya da dama na dakon yin Sallar Idi ranar Lahadi bayan cike azumi Talatin ranar Asabar.

A ranar Juma'a ne dai aka sa ran ganin jaririn watan Shawwal wanda zai bayar da dama a gudanar da Sallar Idi a ranar Asabar.

Sai dai a ƙasar, Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya umarci 'yan ƙasar da su yi azumi talatin sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal.

A wani bangaren ƙasar Saudiyya da wasu ƙasashe ba su ga jaririn watan Shawwal ba wanda hakan ya sa su ma suka cike azumi 30.

Sai dai Jamhuriyyar Nijar ta gudanar da Sallar Idi a ranar Asabar inda ta sha bamban da sauran ƙasashe domin kuwa har Shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou ya halarci Sallar Idi.

A Najeriya ma, wasu sassa na ƙasar sun gudanar da Sallar Idi sakamakon iƙirarin ganin watan Shawwal da suka yi, cikin jihohin kuwa har da jihar Bauchi.

A duk shekara, akan samu rabuwar kai ta ranakun da ake yin Sallar Idi musamman a Najeriya, sai dai wannan karon, da alama an fi samun ruɗani sakamakon yadda wurare da dama mutane sun ajiye azumi a 29.