Bai kamata Facebook 'ya bar Trump na yaɗa ƙarya a shafinsa ba'

Mark Zuckerberg

Asalin hoton, AFP

Wani ayarin masu ilmin kimiyya fiye da 100 sun ce bai kamata Facebook ya bari Shugaba Trump ya yi amfani da dandalinsa wajen yaɗa bayanan ƙarya da kuma tunzura jama'a ba.

Masanan na aikin bincike-bincike ne a ƙarƙashin wani shirin da mai kamfanin sada zumuntar, Mark Zuckerberg tare da mai ɗakinsa ke ɗaukar nauyi.

A cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa, masu binciken sun nuna rashin amincewarsu da kalamin Donald Trump na "idan aka fara wawar dukiya, a lokacin ne bindiga kan tashi".

Kalaman waɗanda shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, suna hannunka mai sanda ne ga masu zanga-zangar da ta ɓarke a faɗin ƙasar bayan mutuwar George Floyd.

Wakilin BBC ya ce tuni dai Mista Zuckerberg ya fuskanci irin wannan suka kan wannan al'amari daga ma'aikatan kamfaninsa na Facebook.

Su dai masu binciken na cewa dandalin sada zumuntar ya gaza wajen yin aiki da manufofinsa, ta hanyar barin Trump ya yaɗa irin waɗannan kalamai.

Zuckerberg dai zuwa yanzu ya ƙi cire rubutun, amma ya ce zai yi nazari kan zaɓin da ke akwai don sanin yadda zai tunkari lamarin.

Kamfanin Tiwita ne ya fara sa zare da Shugaba Trump. Inda ya tantance rubuce-rubuce biyu da shugaban ya wallafa cikin makon jiya inda ya yi gargaɗin cewa aya daga cikinsu na kambama tarzoma.

Shi dai, Mark Zuckerberg ga alama ya tsaya kai da fata kan ƙudurinsa na zuƙewa yaƙin shafukan sada zumuntar.

Sai dai lamarin ya janyo masa fuskantar tawaye daga ma'aikatan kamfaninsa da farko.

Wasu ma'aikatan sun bayyana rashin gamsuwarsu a bainar jama'a, abin da ya har shugaban Facebook ɗin ya ga buƙatar yin taro don yi wa ma'aikatan nasa ƙarin bayani.