Abida Nijar: Yadda 'yar jarida ta mayar da waƙa sana'a

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Mawaƙiya Abida Illo

Wata matashiya a jamhuriyar Nijar Abida Illo, wadda ta shafe sama da shekara 12 tana aikin jarida ta ce ta zaɓi mayar da waƙa sana'a ganin yadda waƙa ta zama zamani da ganin yadda jama'a suka fara yin "baya-baya da yin fina-finai da waƙokin siyasa da harkar sarauta."

Ta ce a matsayinta na 'yar jarida da ke da baiwa a harkar waƙa, ta ga dacewar ta ba da gudummawa a bangaren "tun da ina da basira da fasaha".

Ta ce fara waƙa bai sa ta ajiye aikinta na jarida ba har sai da ta yi aure, abin da ya sa ita da mijinta suka yanke shawarar yin waƙa tare bayan da suka yi yarjejeniya.

Abida ta ce ta shafe tsawon shekara 10 tana waƙa kuma ta fara ne tun lokacin waƙa a dandali "a cikin unguwa da mu da abokanmu, sai mu je mu yi ta yi muna rerawa, ko ki yi wa saurayinki ko kuma mu yi tsakaninmu, haka dai, lokacin ina zaune ma a daki ni kadai ina yi."

Waƙar Duniya Labari, na ɗaya daga cikin waƙoƙin da Abida Illo ta rera wadda ta ce waƙa ce ta nasiha kan rayuwar zaman duniya.

"Kamar yau in mu ne, gobe ba mu ne ba, idan ka dauki wani kamar ko ka raina shi ka dauke shi a kaskance, Allah ba don ba ya son shi ba ne bai mishi haka ba, kai kuma da ya mai da ka haka ba don ya fi sonka ba ne ya mai da ka haka."

Ta ce tana waka a bangarori dama kamar shaye-shaye da matasa ke yi.

A cewarta, waka ta yi mata rana yadda ta samu zuwa kasa mai tsarki sannan ta yi mota da gina gidan kanta.

"Alhamdulillah, inda wani ba zai iya shiga ba, ni zan iya sa kafa ta, darajar wakata a ba ni dam

a na wuce." in ji mawakiya Abida.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Labarai masu alaka