Albarkatun Ƙasa: Abubuwan da suka kamata ku sani game da ma'adinan jihar Zamfara

many of dem di make between 10-50 thousand everi moonth

Ziyarar da gwamnan jihar Zamfara da ke Najeriya, Bello Matawalle, ya kai wa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ranar Litinin inda ya je masa da samfur-samfur na ma'adinan da ke jiharsa ta ƙara fito da muhimmanci haƙo ma'adinan da ke faɗin ƙasar.

Masana harkokin ma'adinan ƙarƙashin ƙasa sun daɗe suna kira ga mahukuntan ƙasar su mayar da hankali wajen haƙo ma'adinan da ke jihohin ƙasar, domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga.

Hasalima, wasu na gani idan ƙasar ta dogara da harkar noma da kuma haƙo ma'adinai za ta tserewa ƙasashe da dama na duniya a fannin tattalin arziki.

Najeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka da ke da tarin albarkatun ƙasa. Ƙasar na da ma'adinai kala-kala kama daga man fetur, wanda ƙasar ta fi dogara da shi.

Baya ga man fetur, akwai duwatsu masu daraja kamar zinare da kwal da lu'lu' (diamond) da azurfa (silver) da dalma (zinc) da tama (iron ore) sai dai har yanzu ba a kai ga gano da dama daga irin waɗannan ma'adinai ba da ke binne a ƙasar.

Ƙasashe da dama na amfani da albarkatun ƙasarsu wajen bunƙasa tattalin arzikinsu ta hanyoyi da dama.

A cewar shafin kundin bayanai na intanet, Wikipedia, haƙon ma'adanai shi ne kashi 0.3% na arzikin da Najeriya ta samar. Rashin haƙo albarkatun ƙasar ya sa Najeriya na shigo da ma'adinai daga wasu ƙasashen da za ta sarrafa su a cikin gida.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya tun bayan da ƙasar ta sami man fetur a 1970, yanzu haka hankali ya fara karkata ga arzikin ƙarkashin ƙasa wadanda ba a mayar da hankali a kan su ba a baya.

Kowace jiha a Najeriya na da nata albarkatun ƙarƙashin ƙasar da Alllah Ya hore mata.

Mun duba nau'ukan ma'adinan da jihar Zamfara take da su da kuma irin dumbin damarmakin da jihar za ta iya samu sanadinsu (albarkatun ƙasar).

Dr Nuruddeen Isa, kwamishinan muhalli da ma'adanai a Zamfara, ya ce jihar na daga cikin jihohin da Allah Ya bai wa albarkatun ƙasa a Najeriya.

Ya bayyana cewa tun 1933 aka fara harkar ma'adanai a jihar ta Zamfara kasancewarsu fitattu wajen haƙo zinare da azurfa da sauran ma'adanai.

"Kusan ƙananan hukumomin jihar 14, babu inda babu ma'adanan nan a cikin jihar nan amma waɗanda suka fi yawa sun fi yawa a Bukkuyum da Anka da Kauran Namoda da Tsafe da Maru da Kadauri da Kwali." in ji Dr Isa.

Ma'adanai a Jihar Zamfara

Kwamishinan muhalli da ma'adanai na jihar ya ce baya ga zinare da azurfa, akwai dumbin albarkatun ƙasa irinsu "sapphire wanda ake sarrafawa wajen yin sarkoki akwai su copper ana samunsa a ƙananan hukumomi 11 a jihar akwai kuma duwatsu waɗanda ake iya yankawa a yi tiles da su."

Ya ce zai yi wuya a iya ƙididdige yawan ma'adanan da jihar Zamfara take da su.

"Cikin 2003 zuwa 2004, an yi wani babban aiki da wani kamfani muka je muka ƙididdige duk inda ma'adanan jihar Zamfara suke a cikin ƙananan hukumomi 14. Kuma mun nemi wurare 37, muka nemi lasisi a wajen gwamnatin tarayya ta ba da dama, an nuna cewa waɗannan wuraren suna cikin wuraren da suka fi ko ina yawan ma'adanai a faɗin ƙasar nan," in ji shi.

Dr Isa ya kara da cewa wuraren suna daga cikin waɗanda suka fi kyau a ma'adanai a Najeriya.

Ga jerin wasu ma'adinan da Allah ya horewa jihar Zamfara:

  • Zinare
  • Azurfa
  • Sapphire
  • Copper

Haddasa rashin tsaro

Kwamishinan ya ce "tun da kusan shekara biyu an tsayar da aikin ma'adanai mun yi ƙoƙarin mu sa duk masu aikin ma'adanai a jihar Zamfara a ɗauke su aiki, wanda idan suka yi jiha za ta riƙa saya ko ta riƙa faɗa musu inda ya kamata su kai su ba wai a bari kowa ya yi abin da ya ga dama ba."

A cewarsa: "Yana cikin abin da ya ƙara haddasa mana rashin tsaro a jihar saboda mutane da yawa suna zuwa daga ƙasashe daban-daban suna aiki, amma idan aka bi ƙarƙashin wannan za a iya sanin wane ke aiki, ina yake yi, me yake samu kuma ina yake sayar da shi."

Ya ce babu ƙiyasi na abin da gwamnatin jihar take samu daga ɓangaren ma'adanai saboda an hana haƙo su sai dai "wanda ta ga dama ta saya ko ta sa aka yi."

"Mun dai kashe dumbin kuɗi na ƙokarin mu haɓaka mu tabbatar da tsarin ya yi kyau amma babu kwabo da gwamnatin Zamfara take samu kan ma'adanai na Najeriya. Cikin ma'adanan da ake da su a Najeriya, kusan kashi 30 zuwa 48, muna da su a jihar nan," in ji Dr Isa.