Coronavirus: Yadda ake sake sarrafa takunkumin fuska da kayan kariya a Kenya

Coronavirus: Yadda ake sake sarrafa takunkumin fuska da kayan kariya a Kenya

Wata 'yar kasar Kenya ta soma sarrafa takunkuman fuska da kayan kariyar da ake sanyawa don hana kamuwa da cutar korona.

Mrs Catherine ta dauki matakin ne bayan da ta ga wasu suna sake amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.

Ta kara da cewa yin amfani da inji wajen sake sarrafa kayan don yin amfani da su a wani bangaren zai kawar da kasadar kamuwa da cutar korona.