Yadda harin kunar bakin wake ya kashe farar hula a Somaliya

Jami'an sojin Somalia sun kwashe shekara da shekaru suna gumurzu da mayakan Al Shabbab

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an sojin Somalia sun kwashe shekara da shekaru suna gumurzu da mayakan Al Shabbab

Mutane uku sun mutu yayin da bakwai suka jikkata lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tada bom din da ke jikinsa a wani gidan cin abinci a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Jami'ai sun ce daga cikin wadanda suka mutu har da karamin yaro.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin.

Kungiyar masu ikirarin jihadi ta al-Shabab, na yawan kai hari ga farar hula da sojoji a kasar.

A ranar Litinin wani dan kunar bakin wake ya kashe sojojin Somaliya 5 tare da jikkata wani mai ba da shawara na sojan Amurka a wani kauye da ke wajen garin Kismayo mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin kasar.

A karshen watan Agustan da ya wuce ne fararen hula goma da wani jami'in dan sanda suka mutu lokacin da al-Shabab ta kai hari kan wani babban otal a gaban-bakin teku a Mogadishu.