Firaminista Fayez Al Serraj: Zan miƙa mulki a watan Oktoba

Mayakan da ke biyayya ga jagoran 'yan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar sun ce sun karbe ikon garin Sirte.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mayakan da ke biyayya ga jagoran 'yan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar

Firaminista Fayez Al Serraj na Libya ya ce yana shirin miƙa mulki ga wata sabuwar hukumar da ake sa ran za ta fara aiki a karshen watan Oktoba.

Mista Serraj ne ke shugabantar gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke mara wa baya a Trabulus. A cikin makonnin da suka gabata aka koma kan shawarwarin warware matsalolin siyasar ƙasar ƙarkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniyar.

Ƙasashen duniya sun sabunta ƙoƙarin da suke yi na samar da mafita ga rikicin siyasar Libya - inda ake tattaunawa domin neman sasanci a ƙasashe dabam-dabam.

A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin a jiya Laraba, Firaministan ya nemi kwamitin da ke shirya zaman sasancin da ake yi da ya hanzarta kafa sabuwar majalisar ministoci da za su maye gurbin gwamnatinsa domin a sami miƙa mulki cikin sauƙi.

Ya kuma ce da gaske yake kan batun miƙa mulki ga sabuwar majalisar ministocin a ƙarshen watan Oktoba.

Sai dai bai fayyace abin da zai yi ba idan aka gaza cimma dukkan matakan miƙa mulkin gabanin ƙurewar wa'adin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yaƙin basasan da aka gwabza a Trabulus an yi shi ne tsakanin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai

Mista Serraj ya bayyana fatan sa cewa mambobi kwamitin za su kammala aikin da aka ɗora mu su kafin watan Oktoban ya ƙare domin a zaɓi sabuwar majalisar shugabancin ƙasar da kuma sabon firaminista.

An naɗa Fayez Serraj ga muƙamin firaminista ne, kuma shugaban majalisar da ke jagorantar ayyukan mulki a ƙarƙashin wata yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da aka kulla a birnin Skhirat a watan Disambar 2015.

Yarjejeniyar ta biyo bayan yaƙin basasan da aka gwabza a Trabulus tsakanin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da kuma abokan gabansu da ke yammacin Libya.

A wancan zamanin, ƙasar ta kuma sake darewa gida-gida inda wasu ƙungiyoyin suka kafa ta su gwamnatin a gabashin ƙasar.