Chaima: Ana bore kan fyade da kisan matashiya a Aljeriya

Boren ya biyo bayan fyade tare da kisan da a ka yi wa wata matashiya a ranar Larabar da ta gabata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gudanar da zanga zanga a garuruwa da dama a Aljeriya, inda a ka bukaci a kawo karshen cin zarafin da a ke yi wa mata.

An gudanar da zanga zanga a garuruwa da dama a Aljeriya, inda a ka bukaci a kawo karshen cin zarafin da a ke yi wa mata.

Boren ya biyo bayan fyade tare da kisan da a ka yi wa wata matashiya a ranar Larabar da ta gabata.

An tsinci gawar Chaima mai shekaru 19 a wani gidan mai da ke da nisan kilomita 80 daga birnin Algiers a cikin wannan watan.

Yanzu haka a na tsare da wanda ya amsa kisan matashiyar.

Akwai ma rahotannin da ke cewa an koma tsintar gawar wata mata a wani daji a daren jiya

Mata da dama sun gudanar da wani zaman dirshan musamman a biranen Algiers da Oran, inda su ka rika kiran sunan 'Chaima', da kuma kira da kawo karshen cin zarafin da a ke yi wa mata.

Haka ma masu fafutuka sun rika rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta da maudu'in #JeSuisChaima.

Asalin hoton, Chaima

Bayanan hoto,

An tsinci gawar Chaima a kone

A cewar mahaifiyar Chaima, wanda a ke tuhumar ya yi yunkurin yi wa yar'ta fyade a shekarar 2016, a lokacin tana shekaru 15, to amma sai a ka yi watsi da karar a lokacin.

Kungiyar kare hakkin mata a Algeria ta Femicides ta ce daga farkon shekara zuwa yanzu an kashe mace 38 a harin ta'addanci mai nasaba da jinsi.

Femicides ta ce ko a shekarar 2019 an kashe wasu 60, kuma kungiyar na da tabbacin adadin ya fi haka ganin cewa ba duka a ka gano ba.