Turkiyya : Erdogan ya ja kunnen masu fafutukar kare ƴan luwaɗi a Turkiyya

Asalin hoton, Google
Shugaban ƙasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kakkausar suka ga ƙungiyoyin fafutukar kare haƙƙin masu ƴan luwaɗi a kasar bayan ɓarkewar zanga-zangar dalibai.
A wani saƙon bidiyo da ya watsa wa mambobin jam'iyyarsa ta AK Party masu ra'ayin riƙau, ya nuna muhimmancin tarihin Turkiyya da kuma hankoron mutanen da ya kira masu yaɗa ɓarna na lalata sunan ƙasar a idon duniya.
Yana magana ne a lokacin da ƴan sanda suka matsa zuwa harabar Jami'ar Boğaziçi ta Istanbul don daƙile zanga-zangar daliban da ke adawa da kame wasu masu rajin kare hakkin ƴan luwadi.
An zargi masu gwagwarmaya da tunzura kiyayya bayan sun nuna hoton wani wuri mai tsarki a Makka tare da tutar bakan gizo ta masu kare yan luwadin.
An kwashe ɗalibai da yawa yayin artabu da 'yan sanda.
A kasar Turkiyya, an haramta luwaɗi da maɗigo, amma duk da haka masu wannan ra'ayi na ci gaba da matsa lambar halatta shi.
Shugaba Tayyip Erdogan, wanda jam'iyyarsa ta ƴan mazan jiya kuma masu ra'ayin addinin musulunci ce, ya ƙi amincewa da bukatar tasu, da ƙin amincewa a sanya harkokin addinin gargajiya cikin kundin tsarin mulkin kasar, sai dai ya bai wa ƴan kasar damar gudanar da addinan da suke yi cikin bainar jama'a ba tare da tsangwama ba.
Sai dai ana zargin shi da ƙarawa kansa ƙarfin iko cikin shekarun da suka wuce.