An gano gawarwakin matasa 12 da suka nutse a teku a Ghana

Ghana
Bayanan hoto, Bakin teun Ghana

Ma'aikatan ceto sun gano gawarwakin yara 12 da suka nutse kusa da bakin teku da ya yi fice a kudancin Ghana.

Suna cikin yara masu shekaru 14 da 17 da suka je ninkaya a ranar Lahadi a garin Apam.

Iyaye da mazauna garin sun taru a gaban tekun domin neman jin labarin wadanda suka bata.

"Na neme shi a yammacin Lahadi amma ban same shi ba, ban iya bacci ba amma daga baya na ji cewa wasu yara sun nutse kuma an tsamo gawarwakinsu. Don haka na wuce can inda na same shi a cikinsu," in ji wani mahaifi.

Wata mata ta ce an gano wasu gawarwaki a ranar Litinin yayin da wasu a ranar Talata.

An rufe bakin teku a Ghana domin daƙile bazuwar annobar cutar korona sai dai an ce yaran sun bi wata hanya ne domin kada a hana su zuwa wurin.

An ajiye gawarwakin mamatan a wani asibiti da ke garin na Apam.

Wani jami'i a hukumar yawon bude ta kasar ya ce abu ne mai wuya 'yan sanda su iya gadin gabar tekun kasar mai tsawon kilomita 540.

Yin iyo a duk wani bangare na bakin tekun Ghana na da hatsari sosai saboda ana samun ruwa da ke zuwa da karfin gaske, sai dai akasarin bakin tekun da ke kasar ba su da jami'an tsaro ko tutocin da za su ankarar da mutane game da hadarin da ke wurin.