NLC: Kungiyar ƙwadago a Najeriya ta yi zanga-zanga kan ƙarin albashi

Ƙungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi gangami a sassan ƙasar kan batun albashi mafi kankanta a Najeriya
Ƙungiyoyin kwadagon sun nuna rashin amincewarsu ne da wani yunkuri da suke zargin ƴan majalisar dokokin ƙasar da yi na zartar da wani kudurin doka da zai bai wa gwamnatocin jihohi zabi wajen biyan albashi mafi kankanta a kasar.
Dubun-dubatar ƴan kungiyar ne suka yi tattaki zuwa majalisar dokoki, suka mika korafinsu a birnin tarayya Abuja.
Sun jaddada cewa ba su da wata bukata face a yi watsi da kudurin.
Shugaban ƙungiyar kwadagon na kasa, Kwamred Ayuba Wabba shi ne ya jagoranci gangamin, kuma wanda ya gabatar da ƙorafinsu ga wata tawagar `yan majalisar dattawa da wakilai da suka wakilci shugabannin majalisun biyu.
Sakonmu ga zauren majalisa shi ne ba mu amince da ƙudirin da aka shigo da shi ba," in ji Wabba
NLC ta ce ta yi mamakin inda suke neman cewa a maganar mafi kankantar albashi a bar wa gwamnoni a jihohinsu su aiwatarwa da abin da ya shafi karin albashi.
A nata ɓangaren majalisar dokokin Najeriya ta ce ta ji kuma ta karɓi ƙorafin ƙungiyoyin ƙwadagon.
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Hon Ado Doguwa ɗaya daga cikin tawagar `yan majalisar da suka tarbi gangamin ƙungiyoyin ƙwadagon ya ce ranar Talata za a tattauna tsakaninsu da ɓangaren zartarwa.
ƴan kwadagon sun ce wannan gangami na gargadi ne kawa inda suka ce ba zu su amince da aniyar `yan majalisar ba, suna alwashin cewa uwar kungiyar kwadagon za ta umurci `ya`yanta su shiga yajin aiki na kasa baki daya idan ba a saurare su ba.
Ƙungiyoyin ƙwadagon na son a bar tsarin yadda yake kamar yadda suka cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya tun a watan Oktoban 2018, cewa wajibi ne ga jihohi su biya naira dubu talatin a matsayin albashi mafi kankanta ba.
Binciken da wakilin BBC ya yi a tsakanin wasu `yan majalisar dokokin Najeriyar ya nuna kudurin da suke shirin zartarwa bai ci karo da muradan 'yan kwadagon ba.
`Yan majalisar sun yi ikirari cewa, kudurin yana nema ne ya ga an cike gibin da ake samu tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya ta fuskar biyan albashi mafi kankantar, ta yadda gwamnatin tarayya za ta iya tallafa wa jihohin da suka gaza wajen biyan sabon albashin daga bisani sai a warware a hankali.
Amma 'yan kwadagon, ga alama ba su gamsu da wannan hanzarin ba.

A watan Oktoban 2018 ne uwar kungiyar kwadagon Najeriyar ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya a kan albashi mafi kankanta na naira dubu talatin.
Tun daga wancan lokacin wasu jihohin suka fara biyan ma'aikatansu, yayin da wasu kuma suka daidaita a kan wani adadi, saboda a cewarsu ba su da sukunin biya tun da ba su da gashin gwamnatin tarayya.
Suna cikin irin wannan daidaitawar ce aka fada cikin bala'in annobar cutar korona.
Annobar cutar korona ta nakasa hanyoyin samun kuɗin shiga ga jihohin ƙasar da dama, abin da ya sa mafi yawansu ba sa iya biyan mafi ƙarancin albashin naira dubu talatin cikin sauƙi.






