Ku San Malamanku tare da Malam Jamil Muhammad Sadis

Bayanan bidiyo,

Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dr Jamil Muhammad Sadis

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Malam Jamil Muhammad Sadis:

Wani malamin addini a Najeriya Jamil Muhammad Sadis ya ce babu abin da ya taɓa faranta masa rai a duniya kamar mafarkin da ya yi da Annabi Muhammad, SAW.

Ya ce duk bakin ciki da damuwa da yake ciki a duniya idan ya tuna mafarkin yana sa masa farinciki da hawaye.

Ya ce mafarkin yana girgiza zuciyarsa da sanyaya masa zuciya duk lokacin da ya tuna.

Sannan wani abin da ke sa shi farin ciki bayan wannan sai wata gasa da suka taba yi a Madina bayan zanen cin mutunci ga annabi, to mutum sama da dubu biyar suka shifa takarar sai dai shi ya zama na daya.

Ya ce manzon Allah ya gina masa gida, saboda da abin da ya samu a wannan gasar ya saye gidansa na biyu.

Tarihin rayuwarsa

Malamin ya ce an haife shi a layin Rediyo da ke tundun wada Zariya ranar 17 ga watan 8 a shekara ta 1980

Kuma a nan ya tashi ya yi rayuwa da karatu. Ya ce mahaifinsu ya taka rawa sama da yada ake tunani wajen iliminatar da su a matakin farko.

Ya soma ne da makantar dare a nan Zariya da kuma na la'asar kuma bayan ya kammala karataun sakadaren sai ya tafi birnin Madina a 1999, idan ya shiga tsangayar ilimin kura'ani da fasahohinsu kuma duk anan ya yi digiri na ɗaya har zuwa na uku.

Sannan daga baya ya tafi birnin Landan inda ya kanatar harkar kasuwanci duniya da tsare-tsaren ayyuka tsakanin 2016-2017.

Daga nan ya je wani gari da ke kusa da Newcastele a Ingila inda ya karanta harkar tattali kan musulunci da tsare-tsare.

Yanzu haka Dr. Sadis shi ne mataimakin darakta kan harkokin kudi a American University of Nigeria, Yola.

'Tun ina yaro son Al-Kur'ani ya shige ni'

Malam Sadis ya ce son sa da Al-kur'ani ya samo asali ne tun yana yaro da kuma rawar da mahaifinsa ya taka a rayuwarsa.

Ya ce "a galibin lokouta tsakiyar dare mahaifina ke tashina daga bacci ya ce na saurari karatun kur'ani, wanda hakan ya taimakamun wajen son kur'ani.

Da farko da kamar wuya wani lokaci nayi da gyan-gyanɗi, har abin ya zame mun jiki, idan ban ji karatun ba bana iya bacci".

Sannan musabakar ta taka rawa sosai a rayuwarsa don suna zagaye gari-gari har akwai lokacin da shi kansa ya shiga musabakar a 1998. Dukka hakan na da alaka da abin da ke zuciyarsa da ƙauna

Malamin ya kuma shaida cewa ya fi son suratun An-Nisaa, haka zalika yana jindadin sauraron Az-Zukhruf da Al-An'aam.

Buri

Ya ce bashi da buri da ya wuce ciyarwa, kuma hakan na faranta masa musamman wanda ba a san cewa shi ya aikata ba.

Sannan yana son ya karanta kur'ani da muryarsa daga farko har karshenta.

Iyali

Yana da mata biyu da ƴaƴa shida

Sannan ƙasar da ya fi sha'awar zuwa ita ce can wata kasa gaba da Denmarki inda ake rana ta wata 6 da dare na wata shida.

A cewar Malamin zuwa irin wadanan wurare na ƙara imani da tsoron Allah.

'Ina kaunar ɗanwake'

Malam Sadis ya ce ɗanwake ne abinci da ya fi so, a baya yana son taliya amma a yanzu ɗanwake ya yi fintinkau.

Ya ce yana farinciki idan aka bashi ɗanwake amma fa mai taushi da tsantsi cakude da dambun kaza.