Cutar kwalara : Yadda cutar ta kashe sama da mutum 60 a Abuja

Ministan Abuja babban birnin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ministan Abuja babban birnin Najeriya

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar kwalara a Abuja babban birnin Najeriya ya kai 66.

Babban daraktan kula da lafiyar jama'a na birnin Dr Sadiq Abdulrahman ne ya tabbatar da hakan ga BBC yayin wata tattaunawa.

Ya ce an samu bullar cutar a dukkanin shiyyoyi shida na birnin, sakamakon gwajin da ake ci gaba da yi wa mutanen da ake kyautata zaton da cutar suka kamu.A cewarsa:

''Tun daya ga watan Mayu muka fara gani alamun wannan cutar, ba a gano kanta ba sai da aka ga mutane suna ta kamuwa, shi ya sa aka yi gwaji aka tabbatar da cewa lallai kwalara ce''.

Ya kara da cewa zuwa ranar Alhamis 22 ga watan Yulin 202, an samu kimanin mutane 873 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

''Ta yadu zuwa dukkanin shiyoyin Abuja, a shiyyar kwaryar birnin watao AMAC an samu mutane 395, sai Gwagwalada da mutane 246, da Bwari da 152, sai kuma Kuje mai mutum 40, da Kwalli mai mutum 37, yayin da aka samu mutum 3 a Abaji'' inji shi.

Likitan ya kara da cewa binciken da suka gudanar ya tabbatar musu da cewa yaduwar cutar na da nasaba da karuwar jama'a da ake samu a birnin na Abuja, amma suna daukar matakai don ganin an hada yaduwar cutar.

Bayanan hoto,

An samu bullar cutar a dukkan shiyyoyi shida na Abuja

Ya ce ''Mun samar da kwamitoci da yawa karkashin hukumomin da ke da ruwa da tsaki wajen yaki da cututtuka a Abuja, kuma ana tura jami'ai kauyuka da garuruwan da ake da barazana, domin a duba irin ruwan da suke amfani da shi da kuma basu shawarwari, baya ga hakan tuni muka kaddamar da sashen bada kulawar gaggawa kamar yadda aka yi lokacin cutar korona''

Karin bayani akan cutar kwalara

A kan kamu da cutar da kwalara sakamakon ta'ammali da gurbataccen ruwan sha da abinci ko kuma kazanta.

Jihohi da dama a Najeriya ne ke fama da bullar amai da gudawa inda har hukumomin lafiya na duniya suka kaddamar da riga-kafin cutar wadda suka ce za ta karade kasashe da dama na Afirka.