Waiwaye: Za a ɗaukaka ƙara kan El-Zakzaky, IPOB ta sha alwashin yamutsa Najeriya

Mun yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya daga ranar Lahadi 25 ga watan Yuli zuwa Asabar 31 ga watan.

Umarnin Kotu na sakin El-Zakzaky

Asalin hoton, IMN

Daya daga cikin manyan labaran da suka faru a makon nan shi ne hukuncin Babbar Kotun Jihar Kaduna na sakin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, jagoran na ƙungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement in Nigeria (IMN) tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin a ranar Laraba daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

"Kotun ta sallame su ne saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja," a cewarsa.

Wakilin BBC a Kaduna Yusuf Tijjani ya ce jim kaɗan bayan bayar da hukuncin ne aka fita da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a mota zuwa gida, inda ba su saurari ko da 'yan jarida ba.

Gargadin da IPOB ta yi wa Najeriya

Kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra ta sanar da aniyarta ta dakatar da dukkan harkokin rayuwa a yankin Kudu maso gabashin Najeriya saboda ci gaba da tsare shugabanta Nnamdi Kanu.

A wata sanarwa da Chika Edoziem, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai rike da mukamin shugaban sashen gudanarwa na kungiyar ya sanya wa hannu, IPOB ta ce ta ba gwamnatin Najeriya kwana 11 ta saki Nnamdi Kanu domin kauce wa killace yankin.

Edoziem ya fitar da wannan gargadin ne kwana biyu bayan da wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ta IPOB ne suka kashe wani babban jami'in 'yan sanda mai mukamin DPO a jihar Imo.

Mista Kanu dai ya tsere ne bayan da wata kotu ta bayar da belinsa a shekarar 2017.

Koken matsalar tsaro da Buhari ya kai wa Birtaniya

Asalin hoton, Presidency

Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya ce a shirye kasarsa take ta taimaka wa Najeriya kan matsalar tsaro da ke damunta.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar ta ce Boris Johnson ya bai wa shugaba Buhari wannan tabbaci ne a gefen taron habbaka ilimi da ke gudana a Landan.

Bayan duban tsanaki da shugabannin suka yi wa matsalar tsaron kasar, sun amince da cewa dole a kyale bangaren shari'a ya yi aikinsa yadda ya kamata.

Duka shugaban sun yarda cewa dole a kyale shari'a ta rika aikinta ba tare da katsa-landan ba, kuma ko da wanene shari'ar ta shafa.

Buhari ya kuma yi wa Firaiministan bayani a takaice kan ikon da Najeriya ke bukatar samu da kuma kokarin da take yi na tabbatar da ta samar da abincin da za ta iya rike kanta da shi.

Ya kuma yi masa bayanin matsalar tsaron da yankunan Najeriya ke ciki.

Mutum 169 da kwalara ta kashe a Kano

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Kano ta ce ɓarkewar cutar kwalara a kananan hukumomi 44 na jihar ta yi ajalin mutane 169, yayinda 191 ke kwance a asibiti.

Darakta a fanin lafiyar al'umma a ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Ashiru Rajab ya shaida cewa an tattaro waɗanan alkaluma ne a cikin watannin uku, sannan ya ƙara da cewa mutum 5,221 suka kamu da cutar, cikinsu 4,860 sun samu sauki.

A cewarsa, mutum 191 da ke kwance yanzu a asibiti na samun kulawa a asibitocin gwamnati.

Dr Rajab ya yi kira ga al'umma da su kula da tsafta da abubuwan da suke ci, musamman mazauna karkara domin kare kai.

Rikicin Abba Kyari da Hushpuppy

Ƴan Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan wata dambarwa da ta barke tsakanin matashin ɗan Najeriya da ke fuskantar tuhuma a Amurka bisa hannu a manya-manyan ayyukan zamba na duniya Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi da kuma shahararren dan sanda Abba Kyari kan zargin bayar da cin hanci.

Ana dai zargin Hushpuppy ne da zambatar manyan kafanonin da ƙungiyoyin kwallon ƙafa da kuma ɗaidaikun mutane a ƙasashensu na fadin duniya.

Wasu bayanai da matashin ya fada wa masu bincike na cewa ya taɓa bai wa jami'in ɗan sanda Abba Kyari wasu kuɗaɗe domin a daure wani abokin huldarsa. Zargin da Kyari ya musanta.

Mutuwar mutum 26 a Kano sakamakon ambaliyar ruwa

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Kano ta ce mutum 26 sun mutu, sannan akwai gidaje sama da 1,000 da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomi hudu da ke Kano.

Shugaban hukumar, Malam Saleh Jiili ya shaida cewa an tattara waɗanan alkaluma ne tun daga watan Afrilu zuwa yanzu, kuma akwai mutum 50 da suka jikkata a ambaliyar.

A cewarsa, kananan hukumomin da aka samu iftila'in sun haɗa da Bunkure da Minjibir da Tarauni da Doguwa.

Ya kuma shaida cewa dama hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen za a samu irin wannan amabaliya a kananan hukumomi 25 na Jihar a wannan shekarar.

Shirin Kaduna na sake shigar da ƙara kan El-Zakzaky

Asalin hoton, Kaduna Govt

Gwamnatin jihar Kaduna na shirin fara sabuwar shari'a tsakaninta da shugaban ƙungiyar Harka Islamiyya a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky.

A ranar Laraba ne wata babbar kotu da ke zamanta a garin Kaduna ta wanke malamin da umurtar a sake shi tare da mai dakinsa Sayyada Zeenat.

Wata majiya a fadar gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce ma'aikatar shari'a ta jihar na aiki kan shigar da karar a yanzu haka.

Sai dai a lokacin da muka tuntubi ɗaya daga cikin lauyoyi da ke kare malamin, Barista Sadau Garba, ya ce har yanzu ba su samu tabbaci game da rana ko lokacin da gwamnatin ke shirin fara sabuwar shari'ar ba.

Haka nan ma mai magana da yawun ƙungiyar ta Harka Islamiyya Ibrahim Musa ya ce suna ganin labarin ne kawai a jarida, amma har yanzu ba a tuntuɓe su game da sabuwar shari'ar.

Sace matar kwamishina a Benue

Asalin hoton, Getty Images

Yan bindiga sun sace matar kwamishinan filaye da tsare-tsare na Jihar Benue da ke arewacin Najeriya, Ann Unenge.

An sace matar ne a Makurdi babban birnin jihar.

Cikin kasa da mako guda ne aka sace wasu matan aure guda biyu a babban birnin, cikin har da matar wani babban likita.

Wadanda suka shaida faruwar lamarin sunce 'yan bindiga sun rika janta a kasa kan su dauke ta karfi da yaji, da misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis bayan dawowarta daga wani kauye Daudu da ke da nisan kilomita 25 daga Makurdi, inda aka ce ta je gaida iyayenta ne.