Bashir Dan Musa: Ina takaicin yadda aka lalata yabon manzon Allah

Bayanan bidiyo,

Ina takaicin yadda aka lalata yabon manzon Allah – Bashir Ɗan Musa

Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Bashir Ɗan Musa:

Fitaccen mawaƙin begen Annabi Muhammad SAW, Malam Bashir Ɗan Musa ya ce yana matukar takaicin yadda aka lalata yabon manzon Allah (SAW) a shekarun nan.

Bashir Ɗan Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce rashin ilimi da kuma son rai ne ya kai masu yabo "suka faɗa duhun jahilci" a wannan lokaci.

"A baya mukan rubuta waƙa mu bai wa junanmu kamar ni da Rabi'u Usman Baba da Rufa'i Ayagi da Bashir Tashi da sauransu, idan akwai kuskure mu gyara wa juna.

"Za a duba idan ka bai wa Annabi haƙƙin Allah sai a gyara, in kuma ka bai wa wani waliyyi hakkin da ba nasa ba shi ma a gyra maka," in ji Malam Bashir.

Ya ce idan kana buƙatar yabon Annabi ba sai ka kushe wanda suke tare da shi ba ko kuma 'yan uwansa annabawa "saboda kowa matsayinsa daban".

"Idan mutum yana so ya yi bege kamar yadda ya kamata a kan turbar gaskiya to sai ya bi sawun magabata.

"An gama duk wani yabo da za a yi wa ma'aiki, mafi kyau sai mutum ya bi turbar da magata suka bi sai a dace. Amma da ka yi yadda kake so to sai ka zame.

"Da akwai waɗanda suke yin yabo karshe ba sa samun ladan komai, saboda ba sa yin sa kamar yadda ya kamata."

Bayanan bidiyo,

Ku San Malamanku tare da Sheikh Abu Ammar

'Tun daga islamiyya muke ƙasida'

Malam Bashir ya ce shi da ire-irensa sun fara yin ƙasida tun suna zuwa Islamiyya.

Iyaye da 'yan uwa sun ba su kwarin gwiwa kan abin da suka sa gaba na yabo.

Dan Musa ya ce ya rubuta ƙasidu da bai san adadinsu ba, saboda tun a wancan lokacin yake rubuta wakokin yabo yana bayarwa ana rerawa.

Mawaƙin ya shahara ne da waƙar "Salli ala khairil wara fagafirlana ya rabbana bi jahi sayyadil wara.

Kodayake da aka tambaye bai ce ita ya fi so ba, amma ya yi murmushi ya ce: "Ita ce ta fi shahara a cikin mutane."

'Babu abin da bege bai yi mani ba'

"Na daɗe ina bege kuma babu abin da bege bai yi mani ba. Wata rana ina bege aka tsayar da ni aka ce an biya mani kujerar Makka [aikin Hajji], zan je in gaishe da fiyayyen halitta," a cewar Bashir Ɗan Musa.

"A ɓangaren yabon auliya'u kuwa, na yi wakata da nake cewa "A gaida kalifar TijjaniSshehu Ibrahim Inyasi". Na yi ta a gaban 'ya'yan Shehu Ibrahim kuma sun yi mani kyauta."

A cewarsa, yabon da ya yi wa wadannan bayin Allah ya sanya shi ne karkashin darajar Ma'aiki, "babu son rai babu neman wata daukaka daga wani in ba masoyinsa ba".

"Yabon ya karbu yanzu a duniya don haka akwai wadanda za mu iya cewa za su gaje mu, amma ina kara jaddada cewa yabo ana yin sa ne kan ilimi."

Mata ɗaya ba ƙari

Bashir Dan Musa ya ce yana da mata ɗaya da 'yaya 10 - maza huɗu da mata shida kuma duk suna raye.

"Babban burina a rayuwa shi ne dawwama a kan tafarkin Ma'aiki, ya'ya da jikoki su tafi suma a kan wannan tafarki."