Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Rabi'u Rijiyar Lemo
Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Muhammad Rabi'u Musa Rijiyar Lemo ya ce babu abin da ke faranta masa rai a rayuwa kamar ya ga ya yayewa mutane damuwarsu.
Sheikh Musa Rijiyar Lemu da ya faɗi hakan a shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, ya ce a lokuta da dama yana burin ganin ya taka rawa da sa wa mutane farin ciki a rayuwarsu.
Malamin ya ce abubuwa da dama na baƙin ciki sun faru da shi a rayuwa musamman rashin iyayensa, domin a waɗannan lokutan ya shiga matsanancin tashin hankali.
Sannan a shekarun da ya kwashe na karatu da wa'azi da tambayoyi, ya fi karɓar korafi ko tambayoyi daga wajen mata kan zamantakewa, musamman tsakanin ma'aurata.
Rayuwar Mohammed Rijiyar Lemu
Sheikh Rijiyar Lemu ya ce an haife shi a ranar 7 ga watan 2 a shekara ta 1975 a ƙasar Saudiyya, amma yana da shekaru biyu a duniya aka dawo da shi Najeriya.
Ya girma a Rinjiyar Lemu domin anan ma ya yi makaranta tun daga matakin naziri da firamare, sannan ya kammala sakandarensa a 'School of Arabic Stuides' ta Kano wato SAS a 1994.
Daga wannan lokaci kuma ya samu gurbin karatun difloma a fannin Hausa da ilimin addinin Musulunci, sai dai bai jima da farawa ba aka ba shi wani gurɓin karatu a jami'ar addini ta Nijar.
Malamin ya ce daga Nijar kuma sai ya sake samun gurbi a Jami'ar Musulunci ta Madina, a can ya samu ya yi karatu mai zurfi a tsangayar hadisi na tsawon shekara hudu.
Bayan kammala karatunsa a Madina ya dawo Najeriya domin yi wa ƙasa hidima wato NYSC, sannan daga baya ya koma jami'ar Bayero idan ya yi digiri na biyu da digir na Uku a ɓangaren addinin Musulunci.
Mutanen da suka yi tasiri a rayuwarsa
Malam Muhammad Rijiyar Lemu ya ce akwai wani ƴayansa da ya taka rawa sosai a rayuwarsa wajen ci gabansa da wasu karance-karancen da ya yi.
Sannan akwai baban yayansa Malam Abubakar Musa Kandahar wanda shima ya koyar da shi da taimaka masa wajen haɓɓakar da ya samu.
Sannan kuma akwai wani babban malaminsa da ya rasu Mal Abdullahi Umar Madabo, shi ma ya koyar da shi, hakazalika ya yi karatu da marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam da dai sauransu.
Malamin ya ce duk waɗannan mutane yana tunawa da su idan ya auna mizani ko matsayin da yake a yanzu.
Wasu na baya da za ku so ku kalla
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Farin ciki da Baƙin ciki
Sheikh Rijiyar Lemu ya ce abin da ya fi sa shi farin ciki a rayuwa shi ne tafiyarsa karatu Madina, saboda labarin ya zo ma sa a lokacin da bai sa rai ba.
Ya ce yana da shekaru 11 a duniya mahaifiyarsa ta rasu a 1986.
Mahaifinsa ya rayu na tsawon lokaci, akwai shakuwa sosai tsakaninsu saboda irin hirarrakin da suke yi.
Rasuwar mahaifinsa ya ɗaga masa hankali sosai da jefa shi cikin kunci da bakin ciki, sannan kuma ya sake shiga wannan yanayi lokaci da matarsa ta fari ta rasu.
Idan kuma yana karatu Suratul Qamar ce wacce ta fi wahalar da shi wajen karatu, amma a duk cikin surorin al-Kur'ani ya fi son Tawba, yana jin dadi karanta shi, in ji Malamin.
Burina da abincin da na fi so
Malamin ya ce ba shi da wani buri na rayuwa sama da mutuwa cikakken musulmi mumini.
Ya yi rubuce-rubuce sosai musamman raddi kan abubuwa da yake da ja a kai, ko yake gani ba a yi daidai ba.
Sannan akwai litattafan da ya fassara zuwa hausa, saboda mutane su fahimta kuma gajerun rubutu yake yi.
Yana sha'awar cin nama sosai, domin baya son cin abinci babu nama, kuma yana son shinkafa da wake ko doya.
Iyali
Yana da mata uku da yara 17, maza 12 mata 5.
Ya yi wasa sosai kuma abin yafi son shi ne wasan motar gwangwani.
Kuma yana ƙaunar kallon ball sai dai bai yarda ta shiga jikinsa ba.
Wasu abubuwan kuma da ke sa shi damuwa su ne, wulakanta danAdam da zulunci da Karya, baya son karya yana son rike alkawari.