Yankin Tigray: Fiye da mutun miliyan biyar na neman agajin gaggawa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi gwamnatin Habasha da hana shigar da kayan agaji yankin Tigray inda mutun miliyan 5.2 ke neman agajin gaggawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi gwamnatin Habasha da hana shigar da kayan agaji yankin Tigray inda mutun miliyan 5.2 ke neman agajin gaggawa

Sojojin Habasha sun ce sun kashe sama da yan tawayen Tigray 5,600 a yaƙin da suke yi a yankin da ke arewaci.

Mummunan rikicin wanda a ke yi tun watan Nuwamban bara ya jikkata wasu ƴan tawayen 2,300 an kuma kama 2,000.

Sai dai sanarwar wadda ta fito daga bakin Janar Bacha Debele ba ta bayyana tsawon lokacin da a ka samu alƙaluman kisan ba.

To amma masu sharhi sun ce wataƙila gwamnati ta tattara alƙaluman ne daga yaƙe-yaƙen da a ka yi a Habasha baya-bayannan.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce miliyoyi na ci gaba da fuskantar yunwa saboda rikicin.

Janar Debele ya zargi ƙungiyar yan tawayen ta Tigray People's Liberation Front (TPLF) da yunƙurin raba Habasha, lura da yadda suka kutsa yankunan Amhara da Afar masu maƙwabtaka.

A cewar Janar ɗin ''ɗaya daga cikin rundunonin ƴan tawayen TPLF ya yi yunƙurin ƙwace iko da yankin Humera mai iyaka da Tigray da Amhara, amma mun ga bayansu.''

To sai dai har yanzu TPLF ba ta yi martani kan iƙirarin sojojin Habashar ba.

A ƙarshen 2020 ne a ka fara yaƙi tsakanin gwamnatin Firanminista Abiy Ahmed da kuma ƴan tawayen Tigray, bayan shafe watanni a na takun saƙa tsakanin gwamnatin da shugabannin na TPLF.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Firanminista Abiy Ahmed

Dakarun Habasha sun kutsa yankin na Tigray da ke arewaci da nufin kifar da gwamnatin yankin, bayan zargin kai wa sansanonin sojoji hari.

A na hasashen cewa an kashe dubbai, yayin da miliyoyi suka rasa matsugunansu inda da dama suka tsere zuwa Sudan.

Sai dai a cewar wakilin BBC a Habasha Kalkidan Yibeltal, ''abu ne mai wuya a iya tabbatar da iƙirarin gwamnati na kashe dubban ƴan tawayen''.

Amma wani abu da babu tababa a kansa shine cewa miliyoyi sun shiga uƙuba da mummunan matsin rayuwa saboda rikicin

A ranar Juma'a Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi gwamnatin Habasha da hana shigar da kayan agaji yankin Tigray, inda ta yi gargaɗin cewa kusan mutun miliyan 5.2 na neman agajin gaggawa.

Majalisar ta ƙara da cewa duniya ta daɗe ba ta shaida tsananin ƙarancin abinci ba kamar wanda ta ke gani a yankin Tigray.