Akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta sauya hanyoyin da take bi wajen magance matsalar tsaro

Akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta sauya hanyoyin da take bi wajen magance matsalar tsaro

Tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta sauya hanyoyin da take bi wajen magance matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar.

A yayin wata hira da BBC, Rabi'u Kwankwaso ya ce har yanzu yana mamakin gazawar gwamnatin Najeriya kuma abin kunya ne a ce har yanzu ana samun yan bindiga da ke sace dalibai a arewacin kasar.

A hirar Kwankwason da abokin aikinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji, sun tattauna kan batutuwa masu yawa ciki har da batun zargin bincikar wasu daga cikin jagororin jam'iyyar su ta PDP da hukumar EFCC ke yunkurin yi, inda ya ce ana kokrin yin haka ne don ɓata musu suna.