Lionel Messi zai buga wa Argentina fafatawa da Brazil

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Koci Lionel Scaloni ya ce watakila Lionel Messi ya buga wa Argentina wasan da za ta yi da Brazil ranar Lahadi a fafatawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Ranar Juma'a Argentina ta kara da Venezuela ta kuma ci 3-1, karawar da aka kori Martinez, sakamakon ketar da ya yi wa dan kwallon Paris St Germain.

Wadanda suka ci wa Argentina kwallayen a ranar Juma'a sun hada da Lautaro Martinez da Joaquin Correa da kuma Angel Correa.

Ita kuwa Venezuela ta zare kwallo daya ta hannun Yeferson Soteldo a bugun daga kai sai mai tsaron raga daf a tashi daga wasan.

Tun farko an ta jita-jitar cewar da kyar ne idan kyaftin din Argentinar zai iya buga wasan hamayya da Brazil a Sao Paulo, sakamakon ketar da aka yi masa.

Scaloni ya ce ''Ina da tabbacin za mu fara wasan da Messi domin yana cikin koshin lafiya, ya yi atisaye lafiyar lau ranar Asabar.''

A cikin watan Yuli, Argentina ta lashe Copa America, bayan da ta doke Brazil mai masaukin baki da ci 1-0, kuma a Sao Paulo.

Tawagar Brazil ce ke jan ragamar teburin kudancin Amurka da maki 21, sai Argentina mai maki 15, sannan Ecuador ta uku mai maki 12, sai Uruguay ta hudu da maki 9.