Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Salah, Rodriguez, Elneny, Mbappe, Onana da Kounde

Asalin hoton, Reuters
Kylian Mbappe
PSG na fatan Kylian Mbappe zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya, duk da tunaninsa na barin ƙungiyar zuwa Real Madrid a baɗi idan kwantiraginsa ta ƙare. (Athletic - subscription required)
A na ci gaba da tattaunawa tsakanin wakilin Mohamed Salah da Liverpool kan ƙulla sabuwar yarjejeniya. (Liverpool Echo)
Akwai yiwuwar ɗan wasan tsakiyar Everton da Colombia James Rodriguez zai tafi kungiyar Istanbul Basaksehir ta Turkiyya kafin a rufe kasuwa ranar Laraba. (Footmercato - in French)
Mai horar da Sevilla Julen Lopetegui ya ce ba da gangan ƙungiyar ta hana mai tsaron bayanta Jules Kounde zuwa Chelsea ba. (Mirror)
Ɗan wasan Arsenal da Egypt Mohamed Elneny zai iya tafiya Besiktas da ke Turkiyya, duk da yawan albashinsa zai iya lalata ciniki. (Mirror)
Asalin hoton, Getty Images
Mohamed Elneny
Daraktan wasannin Ajax Marc Overmars ya ce mai tsaron gidan Kamaru Andre Onana da Arsenal ke nema zai iya barin ƙungiyar idan kwantiraginsa ta ƙare baɗi. (Team Talk)
Rahotanni a Italiya na cewa ita ma mai riƙe da kofin Serie A wato Inter Milan za ta iya neman Onana don maye gurbin Samir Handanovic mai shekaru 37. (Calciomercato - in Italian)
Akwai yiyuwar Eddie Nketiah ya bar Arsenal zuwa wata ƙungiya kyauta a watan Janairu, bayan da ƙungiyar ta kasa sayar dashi a kakar bana. (Sun)