Sojojin Najeriya sun musanta binne gawawwakin ƴan bindiga a manyan ƙaburbura a Zamfara

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Other

Rundunar sojin Najeriya ta nesanta kanta da wasu hotuna da bidiyo da ake yadawa ta kafofin sada zumunta da ke nuna yadda ake binne gawawwaki a cikin manyan ƙaburbura.

Ƴan ƙasar na danganta gawawwakin da cewa na ƴan bindiga ne da sojojin suka kashe a yaƙin da suke yi da su a shiyar arewa maso yammacin ƙasar.

A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin ta ce ana yaɗa hotunan ne da nufin ɓata wa dakarunta suna.

Hotunan da ake yaɗa wa a kafofin sada zumunta sun nuna waɗansu jam`ian tsaro suna jefa gawawwaki a cikin manyan ƙaburbura, wadanda kuma ake cewa gawawwakin ƴan bindiga ne da sojojin suka harbe a arangamar da suke yi da su a jihar Zamfara da sauran sassan da ake fama da ƴan bindigar a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

"Hedikwatar tsaro ta samu labarin hotunan da ake yadawa, wadanda ba su da dadin gani ko kadan, amma sam ba su da alaƙa da farmakin da sojojin Najeriyar ke kai wa ƴan bindiga," in ji sanarwar da Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar, Manjo Janar Benjamen Olufemi Sawyer ya fitar.

Sanarwar ta jadadda cewa "sojojin Najeriya masu bin doka da ka`idojin yaƙi ne, kuma suna martaba haƙƙokin bil`adama - saboda haka babu yadda za a yi su yi irin wannan kisan, ballantana su boye - saboda haka jama'a su yi watsi da batun."

Ta kara da cewa wannan hotuna da bidiyo ana yaɗa su ne da nufin walaƙanta darajar rundunar ne a idon duniya.

Sawyer ya ce wasu hotunan da ake rubuta wa "Alhamdulillah, Dole Zamfara ta zauna lafiya" da sauran wasu hotunan da bidiyon da ake yaɗawa an yi ne domin nuna hazakar sojojin a aikin da suke a arewa maso yamma da kuma arewa ta tsaki da sauran sassan kasar, "cin fuska ne ga sojojin Najeriya."

"Babu wani abu da ya hada rundunarmu da waɗannan hotuna masu tayar da hankali," kamar yadda sanarwar ta jaddada.

Sojojin na samun nasara?

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,

'Yan bindiga da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sanarwar dai ba ta musanta cewa sojojin Najeriya suna samun nssara a kan ƴan bindigar da suke dauki-ba-dadi da su ba, amma ba ta fayyace irin nasarar ba.

Rundunar ba bayar da alƙalumma ba na yawan ƴan bindigar da aka kashe ko aka kama a fagen daga ba.

Sai dai sanarwar ta ce ba ta da wani abin boyewa a cikin gwabzawar da dakarunta ke yi a ko`ina a cikin fadin Najeriya.

Kuma bisa al'ada hedikwatar tsaron Najeriya tana yin bayani a kan nasarori da ƙalubalen da dakarun ke fuskanta a fafatawar da suke yi bayan kowane mako biyu, don haka tana gab da fada wa `yan Najeriya inda da aka kwana a yakin da ke yi da ƴan bindiga shiyyar arewa maso yammacin Najeriya da wasu sassan shiyyar arewa ta tsakiyar kasar.

Kusan kwana 10 kenan da datse layukan waya a jihar Zamfara, kodayake daga baya an datse a wasu sassan jihar Katsina, duka da nufin yi wa ƴan bindigan rufin-ganga tare da daƙile su.

Wannan ya sa sadarwa ta yi wuya a yankin, saboda haka da wuya ake iya tantance gaskiyar abin da yake faruwa.

Wannan ne ya sa ake ta yada jita-jita game da karawar da sojoji ke yi da `yan bindigan.

Kodayake dai mafi yawan labaran da ake yadawa na nuna cewa jami`an tsaron ne ke samun galaba, ko da yake akwai wasu ƙalilan da ke nuna akasin haka.

An saba yaɗa hotunan ƙarya

A mafi yawan lokutan wasu hotuna da bidiyoyin da ake yaɗawa ba na lokacin ba ne, wasu kuma an yi su shekaru masu yawa baya.

A wani abu mafi muni da yake faruwa shi ne, sai a dauko hoton bidiyon da ya faru a wata kasa ta Afrika a alakanta shi da Najeriya.

An ga irin wannan a lokacin zanga-zangar EndSars, inda aka riƙa yaɗa wasu hotuna da bidiyo da aka yi amfani da su a shirin fina-finai.

Rundunar sojin Najeriya ta shawarci 'yan kasar da su rika bin hanyoyin tabbatar da inganci labari gabanin yada shi.

Sawyer ya ce suna da hanyoyinsu da suke fitar da bayanai na nasarorin da suke samu ko akasin haka, ta hanyoyin da suka saba yi.